A yanzu dai duniyar nishadi, musamman a fagen wakokin Hausa, sunan mawaki Ado Gwanja ne yake tashe.
Wannan ya biyo bayan wakoki zafafa guda biyu da mawakin ya fitar a jere: Warr da Chass, sannan kuma yanzu haka ake rade-radin ya kammala shirin sako wata sabuwa, mai suna ‘Girgiza’.
- Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yajin aikin ASUU —Buhari
- Hare-Haren Jirage da Ambaliya Sun sa Boko Haram da ISWAP Gararamba
Wakokin matashin mawakin na shuhura ne cikin kankanin lokaci ganin yadda mata suke yin bidiyon wakokin suna yadawa a kafafen sadarwa.
Aminiya ta lura cewa, ko ’yan mata ne suke hira, idan za su yi shewarsu, tafawa suke yi su yi ihun, ‘Warr’.
Sannan ko a kafafen sadarwa, mata da matasa suna amfani da kalmar Warr din hakanan kawai.
Ado Gwanja ya dade yana nishadantar da mata da matasa, inda a gidajen biki ake yawan amfani da wakokinsa wajen rakashewa.
A kwanakin baya ne Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya (NBC) ta haramta musu sanya wakar ‘Warr’ ta Ado Gwanja kan zargin lalata tarbiyya.
NBC ta ja hankalin gidajen rediyo da talabijin cewa, wakar da shararren mawakin ya yi ta saba Dokar Yada Labarai ta Najeriya saboda tana nuna maye da kuma miyagun kalamai.
Hukumar ta ba da misali da cewa, baya ga nuna yadda ake yin tangadi a cikin wakar, akwai kalamai na rashin tarbiyya a cikin wasu baitocin wakar.
Ta ce, daga cikin baitocin akwai inda mawakin ke cewa, “… kafin a san mu ai mun ci kashin ubanmu…ko kin zo da ke da hodarki ubanku zan ci, ‘warr’ da kuma inda ya ce, Kowa ya ce zai hana mu ubansa zan ci.”
Aminiya ta ruwaito cewa, wadannan baitocin da Gwanja ya yi amfani da su daga wakar Marigayi Mamman Shata ya aro su.
Sashe na 3.38.2c na Dokar Yada Labarai ta Najeriya ta tanadi cewa, “Wajibi ne gidan rediyo ko talabijin ya tabbata ya nuna sanin ya kamata a irin shirye-shiryen da yake gabatar wa al’umma.”
Hakan kuwa na zuwa ne a jim kadan bayan wasu lauyoyi a Jihar Kano sun yi karar Ado Gwanja da wasu mawakan Arewacin Najeriya da ke tashe a kafar Tiktok a kotu bisa zargin lalata tarbiyya.
Aminiya ta ruwaito cewa, lauyoyin sun maka mawakin da sauran mawaka a kotu ne, wanda hakan ya sa kotun ta bukaci ’yan sanda su bincika lamarin.
Sai dai lamarin ya ci gaba da daukar hankali da dama masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum, inda wasu ke cewa ai wakokin Kudu sun fi na Ado Gwanja ‘bata tarbiyya’ amma ba a hana su.
Wasu ma cewa suka yi ana nuna shirin BBNaija da a cewarsu ake nuna fitsara karara, amma ba a hana su.
Matashin dan jaridar nan da ya yi fice a kafofin sadarwa, Aliyu Dahiru Aliyu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Akwai alamun hassada a sako Gwanja a gaba.”
Shi ma fitaccen masanin Adabi, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Malam ba ka ce komai ba game da matsalar Ado Gwanja da hukuma, ko ba aikin adabi ne yake yi ba?” Hmmmm!”
Da take bayani kan batun, fitacciyar ’yar jarida kuma mawakiya wadda take daura muryar Hausa a finafinan Indiya, Mufida Adnan da akafi sani da Moofy ta bayyana cewa, laifin mata ne da suka mayar da wakokin na Gwanja suke komawa kamar na rashin tarbiya.
A cewarta, “Mata ke mai da masa waka ta zamo ta rashin da’a ta hanyar yin rawar rashin da’a.
’Yan kwanakin nan ina yawan sauraran wakokinsa tunda aka fara ce-ce-ku-ce a kansa.
Da farko dai Gwanja mawaki ne sannan yana da damar yin waka yadda yake so yadda ya ga dama haka tasa baiwar take.
“Duk lokacin da ya fitar da wakarsa idan kun kula kafin ya yi bidiyo ya fito mata sun fara yin gasar rawa a TikTok hade da yin rawar rashin mutunci da tabe-taben jikinsu.
“Hasali ma wallahi a duk mawakanmu, Gwanja ne wanda ya fi yawan amfani ni da kalamansa wajen jan hankalinmu a kan iya zama da mutane sannan kuma muke sanin Allah ne mai komai.
“Misali, cikin wata wakar da Dan Musa ya saka shi a ciki, na jima ina lissafi cikin wannan baitin “Ban da Allah wa zai mai da sarki bawa” “Sanin masoyi sai Allah” “A yi kudi da sarauta” “A duniya aka samu” “A duniya za a bar shi.”
Ta kara da cewa, “Akwai wadanda ya kamata a nema a kama ba Gwanja ba. Ban taba haduwa da shi ba, ban san shi ba, bai sanni ba balle ku ce ina magana a kan mun san juna.”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mawakin, amma ba ta samu dama ba.
Sai dai a wata tattaunawa da ya yi da Mujallar Fim ya ce, ba zai ce komai ba game da batun a yanzu.
Sai dai Aminiya ta ziyarci shafin mawakin, inda ta gano yadda mawakin ya ci gaba da tallata wakokinsa, musamman wakar ‘Chass’ da har yanzu ake tsimayin bidiyonta.
Gwanja ya saka bidiyon wani Bature yana wakar ‘Chass’ yana rawar ‘A sosa’, sannan ya rubuta cewa, “Wakar Chass tana nan a kafafen sadarwa na zamani.
“Ku ci gaba da sauraron ta sannan ku ci gaba da yada ta.”