More Podcasts
Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samo daga wurin iyayensa a da can, irin mu’amalan da ke tsakaninsa da iyaye har ma da shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye.
A yanzu kuwa al’amrin ya canza, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa.
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen shi ne aikin albashi da iyaye mata ke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ‘ya’ya suke samu.
- NAJERIYA A YAU: Matakan da manoman Jihar Taraba suka ɗauka kan ’yan ta’adda
- DAGA LARABA: Gudunmawar Da ‘Yan Sa Kai Suke Badawa Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan irin ƙalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyar ’ya’yansu.
Domin sauke shirin, latsa nan