✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin Buhari ya cika alkawuran zabe?

Shin Shugaba Muhammadu Buhari na da abin ce wa ‘yan Najeriya bayan ya shekara biyar a kan karagar mulki? Aminiya ta waiwayi alkawuran yakin neman…

Shin Shugaba Muhammadu Buhari na da abin ce wa ‘yan Najeriya bayan ya shekara biyar a kan karagar mulki?

Aminiya ta waiwayi alkawuran yakin neman zaben Buhari da suka ja hankalin yawancin ‘yan Najeriya suka yi masa ruwan kuri’u.

— Karon farko (Chanji)

A wa’adinsa na farko Buhari ya kayar da shugaban kasa mai ci, Goodluck Ebele Jonathan da gagarumar nasara.

Buhari ya samu kuri’u 15,424,921 shi kuma Jonathan ya samu 12,853,062, a alkaluman da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar.

Yayin yakin neman zaben na watan Maris 2015, Buhari da jam’iyyarsa ta APC sun tallata kudurinsu na kawo ‘chanji’ a Najeriya.

Hakan ya masu jefa kuri’a a Najeriya yin tururuwar zaben sa da mataimakinsa Yemi Osinbajo.

— Wa’adi na biyu (Next Level)

A watan Fabrairun 2019 an sake zaben sa a karo na biyu da kuri’u 15,191,847 bayan ya kayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar dan jam’iyyar PDP da ya samu 11,262,978.

— Mizanin alkawura

Aminiya ta nemi dora alkawuran shugaban da jam’iyyarsa ta APC a mizani domin sanin inda aka kwana.

Mun gano duk da cewa sun shekara biyar daga cikin wa’adinsu na shekara takwas, har yanzu da sauran rina a kaba.

A kundin manufofinta mai taken “Kudurinmu na Sabuwar Najeriya”, APC ta yi manyan alkawura 6 a bangarori da yawa na kasar.

Wakilan Aminiya sun tabbatar da cigaban da aka samu, amma da wuya a iya cewa an kammala cika wani muhimmcin alkawarin.

—Kundin Alkawura

Kundin yakin neman zaben APC ya dora laifin rashin cika alkawuran da jam’iyyar PDP ta yi a kan rashin kundin tsarin alkibilar gwamanati.

Ta ce: “An fara damokradiyya  a 1999 ba tare da gwamnatin ta bayyana wa ‘yan Najeriya muradunta ba saboda ba shirya take ba.

“Rashin alkibilan ya jefa kasar cikin rikice-rikice da siyasar kama karya da koma bayan tatalin arziki.

“Shi ya sa ta shekara 15 ba tare kawo sauyi ba. Jam’iyyar ba ta da wani manufa a kan tsaro da cigaban kasa.

“Za a iya cewa sun yi mulki ba tare alkawarin komai ba kuma ba su aiwatar da komai ba,” inji APC.

— Alkawuran APC sun bambanta.

A kokarinta na shawo kan ‘yan Najeriya su ba ta damar kawo sauyin da ta zargi magabatanta da kasa kawowa, APC ta ce “a baya ana yin alkwuran yakin neman zabe ba tare kawowa a wani daftari da za’a iya bibiyar cika shi ba.

“Mun bayyana a fili cewa za mu cika alkawuranmu idan ‘yan Najeriya suka zabe mu.

Za mu mayar da hankali a kan abubuwa guda shida: tsaro, mulki nagari, cigaban al’umma, cigaba tatalin arziki, ma’adanai da kuma tsare-tsaren hulda da kasashen waje.”

— Ina aka kwana?

Duk da wadannan alkawura, kawo yanzu shekara biyar bayan mulkin jam’iyar, ‘yan siyasa na ganin ba abin da ya sauya zane.

Jam’iyyun adawa musamman PDP na ganin Buhari bai cika alkawuran da ya dauka ba a shekaru biyar da ya yi yana mulki.

Idan aka kwatanta girman alkawuran da gwamnatin jam’iyyar APC ta yi da ayyukanta, to ba abin da jam’iyyar ta yi, a ganinsu.

A nasu bangaren, ‘yan jam’iyya mai mulkin na ganin gwamnatinsu ta yi gagarumin kokari idan aka yi la’akari da halin da suka tsinci kasa a lokacin da suka karbi mulki.