Ga dukkan alamu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dawo kan ganiyarta bayan doke babbar abokiyar hamayyarta da ta yi a wasan mako na 29 na gasar LaLiga.
A yammacin Lahadin da ta gabata ce Barcelona ta lallasa Real Madrid har gida da ci 4 da nema a filin wasa na Santiago Bernabeu.
- Harin sojojin sama ya hallaka shugaban ISWAP, Sani Shuwaram, a Borno
- Ukraine ta sanya dokar hana fita a birnin Kyiv
Nasarar ta bai wa Barcelona kwarin gwiwar rage yawan makin da ke tsakaninta da Real Madrid, kana ta shiga sahun kungiyoyi hudun farko a teburin gasar LaLiga.
Amma duk da haka Real Madrid ta bai wa Barcelona tazarar maki 12, wanda zai iya raguwa zuwa maki tara idan Barcelona ta doke Rayo Vallecano la’akari da kwantan wasan da za ta doka.
Barcelona za ta iya lashe gasar LaLiga matukar Real Madrid ta yi rashin nasara a wasanni uku daga ragowar wasannin da suka rage, sannan kuma idan Sevilla ita ma ta barar da damarta wajen rashin nasara a uku daga cikin wasanninta.
Tauraron Barcelona ya ci gaba da haskawa tun bayan da tsohon dan wasan tsakiyarta, Xavi Hernandez ya karbi ragamar horas da ’yan wasan kungiyar, bayan kungiyar ta raba gari da Ronald Koeman.