’Yan sanda a Jihar Kaduna sun karyata rade-radin da ke cewa ’yan bindiga sun kai hari an kan jirgin kasa da ke hanyarsa ta zuwa Jihar.
An yi ta jita-jitar a yamacin ranar Litinin cewa an kai wa jirgin kasar da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja hari a garin Rijana, wanda ya yi kaurin suna da ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
- Buhari ko Obasanjo: Wa ya raba kan ’yan Najeriya?
- Mun kashe N4.27bn kan harkar tsaro —Gwamnatin Katsina
- ‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro biyu, sun sace 10
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jagile, a bayanin da ya yi wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya ce wasu bata-gari ne a kusa da Rijana suka yi ta yi ta jifar jirgin kasan da duwatsu amma ba hari ba ne.
“Ba harsashi ba ne ko kwari da baka ko miyagun makamai aka harba. Ba hari ba ne, jirgin na tafiya. Jami’anmu da ke Rijana sun shawo kan al’amarin”, inji shi.
Ya ce rundunar za ta yi cikakken bincike kan abin da ya faru kuma duk wanda aka samu da hannu a ciki zai yaba wa aya zaki.
Sai dai ya ce, “Zuwa yanzu babu wanda aka kama amma mun tura jami’anmu domin su gano wadanda ake zargin”.