✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin Allah Yana sonmu? (3)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke…

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki Ranar Sakamako. Kai kadai muke bautawa kuma gare Ka kadai muke neman taimako. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da sauran masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

Bayan haka daga lokaci zuwa lokaci a kamata mu rika yi wa kanmu irin wannan tambaya ta sama saboda halin da mu Musulmi muka samu kanmu a ciki a wannan lokaci. “Shin Allah Yana sonmu kuwa?”
Yin tambayar zai sa mu yi kokarin gano amsa kuma ta haka ne za mu iya gane ko muna tafiya a kan hanyar da Allah Yake so ko a’a. Na fadi haka ne saboda yadda muka iske kanmu a cikin wani yanayi na rana kuna inuwa zafi a kusan duk duniyar Musulmi.
Domin amsa wannan tambaya za mu leka tarihi mu ga yadda rayuwar magabatan kwarai (Salafus Salih) da mamayan kwarai (Khalfus Salih) suka gudanar da rayuwarsu har suka samu daukakar da yanzu muke ta karantawa a littattafan tarihi da na addini, kuma suka zama su ne ke juya duniya a zamaninsu.
Bayan wafatin Annabi (SAW) ba da dogon lokaci ba, Abu Idris Al-Khaulani (wanda ya rasu a shekara ta 80 Bayan Hijira daidai da shekara ta 699-700 Miladiyya) a Damaskus ta kasar Syriya ya tafi Masallacin Al-Kabir. A cikin masallacin ya iske rukunin mutane sun kewaye wani mutum. Ya bayyana siffar mutumin da mutum mai yawan murmushi kuma mutanen sun kewaye shi suna yi masa tambayoyi. Sai Abu Idris Al-Khaulani ya yi tambaya cewa: “Wane ne wannan mutum?” Sai suka amsa da cewa: “Mu’azu bin Jabal ne (RA), sahabin Manzon Allah (SAW).”
Washegari Abu Idris ya sake zuwa masallacin da jijjifi kafin Sallar Asuba, tunaninsa ya zamo mutum na farko da zai fara shiga masallacin. Amma sai ya iske Mu’azu bin Jabal (RA) yana nafila kafin Sallar Asuba. Sai Abu Idris ya isa ga Mu’azu (RA) ya zauna a bayansa ya jira ya idar da sallarsa, Abu Idris ya matsa kusa da shi ya ce: “Ya Mu’azu! Lallai ni ina sonka saboda Allah Madaukaki!” Sai Mu’azu Ibnu Jabal (RA) ya jawo Abu Idris kusa da shi, ya tambaye shi cewa: “Shin da gaske don Allah Madaukaki kawai kake sona?” Abu Idris ya ce: “Eh!”
Sai Mu’az bin Jabal ya yi murmushi ya sake jawo shi kusa ya ce masa: “Zo in ba ka kyakkyawan labari, hakika na ji Annabi (SAW) ya ce: “Allah Madaukaki Ya ce: “Wajabat Muhabbati Li Mutahabina fiya.” Ma’ana “SoyayyaTa ta wajaba ga masu soyayya domiNa.”
’Yan Musulmi! Tarihin dan Adam cike yake da yadda mutane suke cewa suna son Allah Madaukaki kuma Allah Yana sonsu. Kiristoci suna da’awar cewa Allah Madaukaki Yana sonsu, amma sai ga shi Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya kira su da batattu (k:1:7). Haka Yahudawa suna da’awar suna son Allah, amma Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya ce da su: “Wadanda Allah Ya yi fushi da su.” (k:1:7).
To, haka akwai Musulmin da suke da’awar suna son Allah Subhanahu Wa Ta’ala, sai dai abin tambaya shin Allah (SWT) Yana sonsu? Shin da gaske Allah Madaukaki Yana sonmu?
Ya zo a cikin Sahihul Buhari, Annabi (SAW) ya ce: “A duk lokacin da Allah Ya so wani, sai Ya kira Mala’ika Jibrilu Ya ce, “Ya Jibril! Inni uhibbu Fulanu…!” Ma’ana “Ya Jibril! Lallai Ni ina son wane dan wane don haka kai ma ka so shi!” Sai Allah Ya ambaci sunan mutumin, sai Jibril ya so wannan mutum. Sannan Jibril (AS) ya yi shela ga dukkan Mala’ikun da ke cikin sammai bakwai ya ce: “Allah Yana son wane dan wane, don haka ku so shi. Sai Allah Ya sanya son wannan mutum a cikin zukatan mutane!”
To, mu tsaya kowa ya tambayi kansa, me ya sa nake da bakin jini a wurin mutane? Shin me ya sa mutane ba sa sona? Shin idan Allah ana sonmu zai bar mu a irin wannan hali da muke ciki kuwa? Anya yadda muka samu kanmu a yanzu ba alamar Allah bai sonmu ba ne a daidaikunmu da kuma a kungiyancenmu?
A wani Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Bawa ba zai gushe ba yana neman kusanci da Allah; yana neman soyayyar Allah, har sai Allah Ya kira Jibril (AS) Ya ce: masa, “Ya Jibril! BawaNa wane dan wane yana ta kokarin neman yardaTa da kusantaTa. To hakika soyayyaTa ta tabbata a gare shi.”
Alkur’ani da Sunnar Annabi (SAW) sun nuna mana irin mutanen da Allah (SWT) Yake so. Kuma daga cikin mafifitan mutanen da Allah Ya fi so, akwai Annabi Ibrahim (AS). Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce: “Kuma Allah Ya riki Ibrahim a matsayin Khalil (makusanci kuma amini).” (k:4:125). Kuma daga cikin mutanen da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Yake so, akwai Annabi Ayyub (AS). Allah Madaukaki Ya ce: “Mun same shi mai hakuri… Madalla da wannan bawa.”
Akwai abubuwan da ya kamata mu rika yi da za su sa Allah Ya so mu, misali ya zo a cikin Sahihu Muslim inda Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya shaida mana yadda wata rana wani mutum ya tafi ziyartar dan uwansa saboda Allah Subhanahu Wa Ta’ala. A kan hanyarsa ta zuwa, sai Allah Ya aika masa da wani Mala’ika ya tambaye shi inda zai je, sai ya ce: “Zan je ziyarar dan uwana ne saboda Allah Subhanahu Wa Ta’ala.” Sai Mala’ikan ya ce: “Ba ka da wani dalili na zuwa gidansa bayan wannan?” Sai mutumin ya ce: “Ba ni da wani dalili na zuwa sai saboda Allah Subhanahu Wa Ta’ala.” Sai Mala’ikan ya ce: “Hakika ni Mala’ika ne daga Allah Subhaanahu Wa Ta’ala, kuma ina yi maka bushara cewa Allah Yana sonka!”
Za mu cigaba insha Allah