Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jin kai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta, Amin.
Bayan haka, mun kwana a karkashin bayanin cewa Allah Shi ne Mai kaga halitta kuma Ya mayar da ita bayan mutuwarta, a karkashin aya ta 64 (cikin SurarNaml). Ga ci gaba:
Wannan kuma ya yi kama da inda Yake cewa, “Lallai ne damkar Ubangijinka mai tsanani ce kwarai. Lallai ne Shi, Shi ne Mai kaga halitta, kuma Ya mayar da ita (bayan mutuwa).” Surar Buruj, aya ta 12 da 13.
Sai kuma inda Allah Yake cewa, “Kuma Shi (Allah) ne Wanda Ya fara halitta, sa’annan Ya sake ta, kuma (sakewar halittar) ta fi sauki a gare Shi…” Surar Rum, aya ta 27.
Allah Ya ce, “…. Kuma Wane ne Yake azurta ku daga sama da kasa….” Wato ma’ana da ruwan sama da Yake saukowa daga sama, lamarin da yake sa albarkatun da ke cikin kasa (na tsirrai da itatuwa masu bayar da ’ya’ya da kuma wasunsu) su bunkasa. Wannan kamar yaddaYake cewa a wani wuri daban, “Ina rantsuwa da sama ma’abuciyar ruwa mai komawa yana yankewa. Da kasa ma’abuciyar tsagewa.” Surar daarik, aya ta 11 da 12. (A karkashin wannan ne Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, a littafinsa, Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma Zuwa Harshen Hausa, a shafi na 927, ya ce, “Wannan ya yi kama da zuwan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), a cikin Jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi; kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron kasa; hantsar ruwa ta ba da nono saboda jariri; kuma maniyyi ya zo lokacin jima’i.)”
Haka nan Allah Ya ce, “(Allah ne) Ya san abin da yake shiga a cikin kasa da abin da yake fita daga gare ta; da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta….” Surar Saba’i, aya ta 2. A nan, Allah, Tabaraka Wa Ta’ala, Yana zubo ruwa daga sama a matsayin wata albarka, kuma Ya sanya ruwan ya shiga cikin kasa, sannan kuma, a wadansu wurare, sai ruwan ya rika bubbuga (a matsayin marmaro). Bayan nan, a dalilin ruwan saman nan, sai a tsirar da nau’ukan kayan abinci iri-iri da ’ya’yan itatuwa mabambanta da furanni cikin yanayinsu da launukansu daban-daban. Sai kuma Allah Ya ce, dangane da wadannan abubuwa da aka fitar, “Ku ci kuma ku yi kiwon dabbobinku na ni’ima. Lallai ne, a cikin wannan, akwai ayoyi ga masu hankali.” Surar daha, aya ta, 54.
Yanzu duk bayan gani da jin wannan da wani abin da ya yi kama da shi, “Ashe akwai wani abin bautawa tare da Allah?” Lallai Allah Shi ne Ya fi cancantar a bautamaSa da gaskiya, Shi kadai! In kuwa wani ko wasu suna ganin akwai wani wanda ya isa a bauta masa, to, “Ka ce (musu ya Muhammad), “Ku kawo dalilinku (hujjarku a kan haka), idan kun kasance masu gaskiya.” Kuma sanannen al’amari ne, ba su da gaskiyar, sai dai a yi karfin hali, amma ba wani dalili ko wata hujja da (kafirai) za su nuna cewa abin da suke bautawa, ba Allah ba, yana da wani tasiri a cikin lamarinsu. Allah Yana cewa, “Kuma wanda ya kira, tare da Allah, wadansu abubuwan bautawa na daban, ba yana da wani dalili (hujja) game da shi (kiran) ba, to, hisabinsa yana wurinUbangijinsa kawai. Lallai ne, kafirai ba su cin nasara.” Surar Mu’minun, aya ta 117.
Babu shakka Allah Shi kadai Yake cikin kowane sha’ani, a nan duniya, balle kuma Lahira. Shi kadai Ya san abin da yake boye (gaibu); ba Ya da mata kuma ba Ya da da, balle a ce zai gaje Shi, kuma ba Ya da abokin tarayya, balle a ce,wata rana, za a yi sabani ko gogayya da juna ko nuna karfi ko wata gadara ko wani abin da za a ce, ‘na wane ya fi na wane.’ Shi ya sa ma Allah Ya ce, “Allah bai riki wani abin haihuwa (da) ba, kuma babu wani abin bautawa tare da Shi. Idan (kuwa) haka ne, (cewa akwai abin bautawa tare da Shi), lallai ne da kowanensu (abin bautawar) ya tafi da abin da ya halitta (kowa ya kama gefensa), kuma lallai ne da wadansu sun rinjaya a kan wadansu. Tsarki (kubuta daga nakasa, balle samun kishiya) ya tabbata ga Allah, daga abin da (kafirai) suke siffantawa.”Surar Mu’minun, aya ta 91.
Aya ta 65 (Surar Naml), “Ka ce, “Babu wanda ya san gaibi (abin da ke boye) a cikin sammai da kasa face Allah. Kuma ba su sansancewar a yaushe ne ake tayar da su.”
Allah Ya umurci ManzonSa (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fada wa dukkan halittu cewa ba wani daga cikinsu, a sama yake ko a kasa, da ya san gaibi, sai dai Allah Shi kadai! Wannan wata yanke hujja ce sak, babu sassauci ko wani lako-lako, saboda haka, “Kuma a wurinSa (Allah) mabudan gaibi suke, babu wanda yake sanin su face Shi….” Surar An’am, aya ta 59.
Sheikh Abubakar Gumi, a nan ya yi sharhin cewa, (manufa), “Lokacin aukuwar abubuwa na alheri da na azaba da rayuwa da mutuwa da sauransu, babu wanda ya san su sai Allah. Wanda ya ce ya san wani abu na gaibi alhali kuwa, shi ba wani Manzon Allah ba, to kafiri ne. Haka kuma wanda yake cewa, Annabawa sun san dukkan gaibi, kamar yadda Allah Ya sani, shi ma kafiri ne.” (Duba littafinsa, Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma Zuwa Harshen Hausa, a shafi na 196).
Sannan kuma, Allah Ya ce, “Lallai, Allah a wurinSa kawai sanin Sa’a yake, kuma Yana saukar da girgije…. (har dai zuwa karshen ayar)” Surar Sajdah, aya ta 34.
Kai, karshe dai, “Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayarSa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kasa. Lallai Shi ne Ya kasance Masani, Mai ikon yi.” Surar Fadir, aya ta 44. Saboda haka lallai babu abin bautawa da gaskiya bisa cancanta sai Allah, Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a kan haka!
Allah Ya ba mu dacewa a cikin bauta maSa Shi kadai! Wannan shi ne karshen abin da ya samu, sai kuma a makona gaba, in Allah Ya nufe mu da kaiwa, za mu dauki wani maudu’in.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh!
Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah (5)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da…