✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigowar Gwamna Matawalle APC alheri ne — Shinkafi

Ita kanta Jihar Zamfara za mu ga ta canja.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Mahmuda Aliyu Shinkafi ya bayyana shigar Gwamnan Jihar, Bello Mohammed Matawalle Jam’iyyar APC a matsayin alheri.

Alhaji Mahmud Shinkafi ya ce suna da tabbaccin cewa canja shekar da Gwamnan ya yi daga PDP zuwa APC za ta taimaka wajen kawo hadin kai a jihar.

Ya bayyana haka ne a wajen taron gaggawa da Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Abdul’aziz Yari ta yi da masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyar daga kananan hukumomi 14 na jihar a garin Kaduna.

Alhaji Mahmuda ya ce suna ganin da yardar Allah wannan canjin sheka na Matawalle zai zama abin farin ciki ga duk wani dan Jam’iyyar APC a Zamfara.

“Muna godiya ga Allah cewa wannan ci gaba ne da yardar Allah, domin ita kanta Jihar Zamfara za mu ga ta canja kuma za a samu dama iri-iri a siyasa.

Saboda dukkanku da ke nan shugabanni ne kuma ana ba ku bayanin yadda aka yi da abin da za a yi. Saboda haka mun karbe shi hannu biyu,” inji shi.

Shi kuwa Abdul’aziz Yari ya ce duk da cewa hanyar da aka bi wajen janyo Gwamna Matawalle ya shigo jam’iyyar ba a bi yadda ta dace ba, amma sun karbe shi a jam’iyyar suna kuma fatar shigowarsa za ta amfani ’ya’yan jam’iyyar da jihar baki daya.

Ya shawarci ’ya’yan Jam’iyyar APC musamman wadanda ba su ji dadin shigowarsa cikinsu ba da su rungumi abin a matsayin kaddara daga Allah.

Kazalika, ya ba su tabbacin cewa za su kare musu hakkokinsu da kuma ganin ba a cutar da kowa ba.