kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatis Sunnah reshen Jihar Gombe ta bukaci Musulmi su rika ba ’yan agaji cikakken hadin kai yayin da za a bincike su da ababen hawansu kafin su shiga masallaci a ranar Juma’a.
Shugaban kungiyar na jihar Gombe kuma Sakataren Shirye-Shirye na Majalisar ’yan agaji ta kasa, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya yi wannan kira a babban Masallacin Juma’a na kungiyar da ke unguwar Bolari a ranar Juma’a.
Injiniya Salisu ya ba ’yan agaji umarnin su rika gudanar da kwakkwaran bincike a kan kowa da kowa kafin a shiga harabar masallaci, inda aka fara da shi kafin ya shiga cikin masallacin, domin kowa ya yi koyi da shi, sannan don samun kyakkyawan tsaro a lokacin gudanar da sallar juma’ar.
“Ina kira ga daukacin jama’a da su ba ’yan agaji dukkan hadin kan da ya kamata a lokacin gudanar da duk wani taro na addini, don ganin an tantance jama’a, kasancewar ta wannan hanyar ce kawai za mu cimma burinmu na zakulo masu kashe mutane a wuraren ibada.” inji Shugaban.
Ya roki jama’a su yi hakuri da duk wani binciken kwakwaf da za a yi musu, ba komai ba ne ya jawo hakan illa don ganin an gudu tare an tsira tare a wannan lokaci na rashin tsaro.
Daga bisani ya yi godiya ga jama’a kan hakurin da suke yi da ’yan agajin a lokacin da suke gudanar da aikin nasu.
Shiga masallaci: Izala ta bukaci a ba ’yan agaji hadin kai wajen gudanar da bincike
kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatis Sunnah reshen Jihar Gombe ta bukaci Musulmi su rika ba ’yan agaji cikakken hadin kai yayin da za a bincike su…