✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shiekh Maigona: Yadda abokin Pantami ya rasu a Makkah

Maigona shi ke yi wa Pantami wakilci a wasu hidindimu saboda alaka ta kut-kut da ke tsakaninsu.

Shiekh Dokta Abdurraham Umar Maigona, amini kuma makusancin Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya rasu a birnin Makkah jim kadan bayan sauke farali a aikin Hajji na bana.

Shiek Dokta Umar Maigona, yana daga cikin mambobin Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihar Gombe da gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya nada kwanan nan.

Kafin nada shi a hukumar, Sheikh Maigona malami ne a Sashen Nazarin Addinin Islama a Jami’ar Jihar Gombe (GSU).

A wata takarda da Sakataren Hukumar Alhazan Gombe, Alhaji Sa’adu Hassan ya fitar ta hannun Babbar Jami’ar Hulda da Jama’a ta hukumar, Hajiya Hauwa Muhammad, ta nuna cewa malamin ya rasu ne bayan wata ’yar gajeruwar jinya da ya yi.

Kafin rasuwarsa, Shiekh DoktaMaigona ya yi karance-karance sosai na addini tare da Ministan Sadarwar da wani abokinsa, Nasiru Adamu El-Hikaya da ke aiki da Rediyon Muryar Amurka.

A mafi yawan lokuta, duk wata hidima da Ministan zai yi idan bai samu zuwa ba Maigona shi ke masa wakilci saboda alaka ta kut-kut da ke tsakaninsu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an yi jana’izarsa a babban Massallacin harami na Makka.