✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shettima zai wakilci Najeriya a taron CHOGM na 2024

Shugaba Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilci Najeriya a taron kashashe rainon Ingila (CHOGM) na 2024.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, don ya wakilci Najeriya a taron kashashe rainon Ingila (CHOGM) na 2024.

Taron zai gudana ne a Apia daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Oktoba, inda shugabanni daga ƙasashe 56 mambobin ƙungiyar za su halarta, ciki har da Sarki Charles na Ingila.

Taken taron bana shi ne “Makoma Mai Dorewa: Canza Tattalin Arzikinmu,” inda za a mayar da hankali kan yadda kasashen kungiyar za su bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar amfani da fasaha da haɗin kai.

Za kuma a tattauna zaben sabon Sakataren Janar na Commonwealth, tare da ’yan takara daga Lesotho da Ghana da Gambiya, yayin da Najeriya za ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na babbar kasa a Afirka.

Shettima zai yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin masu zuba jari zuwa Nijeriya, inda ake sa ran shugabannin za su tattauna matsalolin da suka shafi duniya.

Kazalika, Shettima zai halarci muhawara kan tattalin arziki da sauyin yanayi da da tsaro, domin nemo mafita da zaman lafiya da makoma mai dorewa ga matasa biliyan 1.5 na ƙungiyar Commonwealth.

Zai kuma yi taro da shugabannin kasashe daban-daban domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban duniya.

Sannan zai yi wata ganawa da shugabannin don nema wa Najeriya mafita kan halin da tattalin arzikinta ya samu kansa.