Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ya tafi Afirka ta Kudu domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen BRICS karo na 15 da za a yi a birnin Johannesburg.
Shettima zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da ’yan kasuwa a faɗin duniya domin halartar taron a Afrika ta Kudu wanda zai gudana daga 22 ga watan Agusta zuwa 24.
- Ba za mu yi karya don kare muradun gwamnati ba — Ministan Labarai
- Cancanta muka duba wajen zaɓo ministoci — Tinubu
Taron zai tattauna ne kan batutuwan da suka shafi kasuwanci, saukaka zuba jari, samun ci gaba, kirkire-kirkire da kuma garanbawul na yadda ake shugabanci a faɗin duniya.
Har ila yau, taron zai duba batun ci gaba da tallafa wa ƙasashen Afrika da kuma Kudancin duniya.
Manyan shugabanni da za su halarci taron sun haɗa da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Shugaba Xi Jinping na China, Shugaban Brazil, Luiz da Silva da kuma Firaministan Indiya, Narendra Modi.
Bayanai sun ce an kuma gayyaci Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka da kuma Shugaban Sabon Bankin Ci gaba.
Kasashen na BRICS dai sun kunshi Brazil, Rasha, China, Indiya da kuma Afirka ta Kudu, waɗanda suka kasance manyan ƙasashe da ke kawo karfi da kuma masu tasowa.
Al’ummar ƙasashen ya kai kashi 42 na yawan al’ummomi a faɗin duniya da kuma ke da kashi 23 na tattalin arziki.