✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shettima ya ƙaddamar da kwamitin ƙarin albashi

Mataimakin Shugaban Kasa ya ƙaddamar da kwamitin mafi ƙarancin albashi mai mambobi 37.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da kwamitin da zai yi nazari kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a Nijeriya.

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Bukar Aji aka ɗora wa nauyin kwamitin wanda aka ƙaddamar a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Da yake jawabi, Shettima ya ce ƙaddamar da kwamitin ya tabbatar da kudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta walwala da jin daɗin ma’aikata a ƙasar.

Ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki tuƙuru cikin gaskiya da riƙon amana wajen tuntubar duk masu da tsaki domin sauke nauyin da aka rataya musu.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin mai mambobi 37, Bukar Aji ya bayyana kwarin gwiwar cewa za su yi adalci wajen gudanar da aikin duba da irin nagartar mambobin da kwamitin ya kunsa.

An dai kaddamar da kwamitin ne sakamakon tashin gwauron zabi da kayan masarufi suka yi biyo bayan janye tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi.

Kwamitin wanda ke da wakilai daga bangaren gwamnati da ’yan kwadago da kamfanoni masu zaman kansu da sauransu zai tattauna ya ba da shawara kan sabon mafi karancin albashin da kuma yadda za a fara biya.

Wasu daga cikin gwamnoni da kwamitin kunsa sun haɗa da Gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago a matsayin wakilin Arewa ta Tsakiya, sai Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi a matsayin wakilin Arewa maso Gabas da Gwamna Umar Dikko Radda a matsayin wakilin Arewa maso Yamma.

Akwai kuma Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra a matsayin wakilin Kudu maso Gabas da Gwamnan Osun Ademola Adeleke a matsayin wakilin Kudu maso Yamma da kuma Gwamnan Kuros Riba Otu Bassey a matsayin wakilin Kudancin Kudu.

Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun 2019 ne Gwamnatin Najeriya ta yi karin mafi ƙarancin albashi na karshe, daga N18,000 zuwa N30,000.