✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sherrif ya kai ziyarar ba-zata a ofishin APC

Tsohon gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sherrif ya kai ziyarar ba-zata a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja. Da yammacin Alhamis ne Sherrif ya isa…

Tsohon gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sherrif ya kai ziyarar ba-zata a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja.

Da yammacin Alhamis ne Sherrif ya isa ofishin jam’iyyar, inda ya shiga daya daga cikin ofisoshin kwamitin riko na Mai Mala Buni da ke shirya babban taro da zaben sabbin shugabannin jam’iyyar.

Sai dai kuma ya ki ce wa ‘yan jarida uffan game da makasudin ziyarar wadda ke zuwa tsawon lokaci tun bayan dawowarsa cikin jam’iyyar daga PDP.

Masu sharhin harkokin siyasa na ganin zuwan nasa wani yunkuri ne na sake dawo da karsashinsa a cikin jam’iyyar gabanin babban taronta na kasa da kwamitin ke shiryawa.