Shugaban Jam’iyyar NGP na Kasa, Dokta Yakubu Shendam ya soki lamirin taron da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da shugabannin jam’iyyun APC da na PDP inda ya yi zargin cewa taro ne na ruguza damokradiyya.
Shendam wanda shi ne sabon Mai Magana da Yawun Kungiyar Gamayyar jam’iyyu Ta kasa ya yi mamakin dalilin da a sa Shugaba Buhari bai gayyaci sauran jam’iyyu 40 taron ba.
“Taron sirrin wanda jam’iyyun biyu suka yi ya nuna karara cewa jam’iyyar APC da ta PDP danjuma ne da danjummai. Muna tattaunawa don ganin mun nemi kadinmu a kotu kan kawancen rashin gaskiya da jam’iyyar APC da PDP suka yi don kasafta jihohi a zabe mai zuwa”. Inji shi.