✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shema ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Gwamna Dikko Radda ne ya karɓi tsohon gwamnan tare da sauran tawagar jam’iyyar a garin Dutsinma.

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya sauya sheka daga jam’yyar PDP zuwa APC.

Gwamna mai ci, Umaru Dikko Radda ne ya karɓe tsohon gwamnan tare da ’yan tawagar jam’iyyar a garin Dutsinma.

Tun kafin zaɓen 2023 dai wasu suka fara hasashen sauya shekar tsohon gwamnan bisa ire-iren matsalolin da PDP ta riƙa shiga a jihar.

Kafin sauya shekar da tsohon gwamnan ya yi, ya turo wasu na hannun damansa da suka koma jam’iyyar APC, lamarin da wasu suka riƙa cewa saura shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, kwatsam a wannan Larabar tsohon ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar ta PDP inda ya koma APC.

An yi ta raɗe-raɗin sauya shekar tun bayan da a watan Agustan bara Shema ya gana da tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Rahotanni sun bayyana cewa, Shema ya ziyarci Ganduje a gidansa da ke Abuja tare da magoya bayansa da mambobin jam’iyyar APC daga Jihar Katsina.