Shigifar shela
Shawo kan wahala
Sha’anin shammatar ’yan shila
Shan kan shamuwar da ta cilla
Shashancin sha’awar shillon shagala
Kasashe na fama da matsala
Wasu na cikin walwala
Dukiyarsu sun tattala
Sai su sakata su wala
Don sun fasko masu kuntunguila
Baba yai balaguro
Zillon Zaman-fara ya zaburo
Magabta na tamnar goriyar goro
Wai sun samu ala-koro
Barkonon tsohuwa ba citta da mosoro
Turakar taron tula tattali
Takaddama mai fasali
Tattaunawar natsuwar hankali
Tantance kasashen da ke da hali
Talauci da tarin dukiya tuli-tuli
Gangamin Amman
Wakilai daga Tunis
Da jin batu su kai mukus
Arewacin Ifrikiyar nan
A taron bararraje tunanin nan
Haurobiya ta samu wakilci
Baba ba ya butulci
Yai ta batun tabbatar da adalci
Cewarsa akwai masu kaurar jahilci
Tantance tsaba da tsakuwa ne bambanci
Haurobiyawa masu kishi
Ai sana’ar na-duke mai armashi
A dundume kururu kowa ya koshi
Mu yunkura mu tashi
Aiki ne ba fashi
A kiwata bisashe
Kar ai kwance rashe-rashe
Da zarar gari ya washe
Malam Bahaushe
Nemi matsabbai ka kashe
Hada-hadar yau da ta kullum
Sai tumbi yai tuntum
In ba maganin tabahuwa sai ai jugum
Wasu sui shiru abinsu kurum
Ko ai ta jimami jim
Lamurran la’akari
Ai wa al’umma tari
A kawar da mura mai sa tari
Kowa ya samu sarari
Mu bar rugumniyar kakari
Fullo ya daina neman burtali
Ko gararambar kwararon lawali
Ko zai biya haraji da jangali
Nagge tai kashi da bawali
Miyagu su daina tsunkuli
Makekiyar makiyaya
Mashayar dabbobi mikakkiya
Mayankar naman miya
Matattarar takin kunya
Masara ta bayar da yabanya
Kaza tai ta kyarkyara
Zakara yai ta cara
Kwayaye sui ta kwarara
Mu tunkude akurki mu tattara
Mui ta ci kwara-kwara
Hauhawar hayaniya yai yawa
Hatsaniya ba kakkautawa
Hayagagar yunkurin yakicewa
Hankoron yagalgalawa
Hakilon hadamar handamewa
Baban-burin-huriyya
Batun Taron tattalin duniya
Ya bijiro da masu cin dunduniya
A Ifirikiyya
Musamman Haurobiya
Kasurar kaura
Kukuta kurda-kurdar sahara
Kaimin kwarara kura
Kawata yin hijira
Kusar karfe ta kaurara
Yai nufin kai ga gaci
Yai nunin lamurran da suka baci
Ya koka da rashin zaman mutunci
Yai nunin da talalar tattalin talauci
Ya daura aniyar zumun zumunci
Aikata aikin aikatau
Ai aikin haye hawa
A farmaki masu hana kwarar ruwa
A lalubo mahangar mirginawa
A magance cikas din fatatakau
Kowa ya samu dama
Ai sai ya dama
Amma safe da yamma
Ba a dama-dama
Aiki ake girma-girma
Tsakiyar Gabashi
Fitintinu sun yi taushi
Tada kayar baya yai yaushi
Akwai tsirarin masu jifar mashi
Taron dangi ya sa sun kwashi kashi
A Arewacin Ifrikiyya
An dakushe tarnakin kiyayya
Ana ta taron gamayya
Ana bunkasa tattalin sanayya
Amma a wajen Larabawan duniya
Mu kyautata zamantakewa
Mu yasar da zaman-tattakewa
Tattalinmu ya zam na kowa-da-kowa
Ba hadama balle kokowa
Kwashi-kwaraf da dukiya na cutarwa
A inganta ilimin kimiyya
Mu samu kyawun kayan miya
Gayaunar hatsi mai yawan yabanya
Mu daure dami kaya-kaya
Sai a tuka tuwo mui ta ciyayya
Kere-keren karfafan kira
Daure-dauren daure damara
Dabarbarun duba dabara
Lallamin lumanar lamura
Kwanjin kasaitar kasura
Firfitowar fetur
Fafatawar fatattaka fafur
Farauta fur
Furkaniyaniyar filfilo fir
Fashe-fashe fasadabur
’Yan dugwi-dugwi
Kar sui na agwagwi
Su rage wargi
Su daina magagi
Dungurawarsu ta zarta dugwi
Mu bi matakin magabata
Managartan mahukunta
Masu yawan kyauta
Martabarsu biya wa al’umma bukata
Manufarsu kawar da kunci a wadata
Haramar hadin kan ’yan uwa
Hantarar ’yan wawa
Masu hargagi da kuwwa
Da ke sanya al’umma tsuwwa
Dole sai an daka musu tsawa
Baba
A mika matakin na-gaba
Al’umma a yasar da giba
A daina gaba
Burinmu hawa matattakalar gaba
Sai ai aiki tukuru
Mu baje na-mujiya kuru-kuru
Na-zomo yai zunguru
Kar a bari kowa ya kwaru
A jajirce don ganin kowa ya karu
A rage sambatu
Da surutu rututu
Mabarnata ban da shigar burtu
Na-zomonmu ya ji wannan batu
Sai rikici ya zamo dan hutu
Zalunci a sa shi a turu
Mu murmure mu moru
Jikkunanmu sun horu
Na-mujiya yai zuru-zuru
Muna ta kallo kuru-kuru
Masu hankali abokan hira
Kui wa al’umma takara
Don jadadda musu kira
Ko da isar da sakon sankira
Don raunana su daina kara
Mu bai wa juna shawara
A daina tufka da warwara
Kasarmu ta rage asara
Kowace jibar jibgin kara
Sai mu daura aniyar shara
Shelar shammatar shan shayin shagala
Gundumar gudunmuwar gutsire gafala
Dumuiniyar durfafar danne dafdala
Carin cakwaikwaiwar cabin cabalbala
Karafkiyar kwakwazon kalle-kalle ku kula
Nai balaguro da mutan Habasha
A natse suke tun a tasha
Mutan Asmara ba sa bushasha
Sawun-diyyar Larabawa ta hana shan kayan kusha
An hana masha’ar aikin assha
Ba tsimi ba dabara
Daukacin matsaloli a tunkara
Mui himma mu yunkura
A bar nuna gadara
Miyagu sun kwanto kura
Birni da karkara
Karfin karafuna su tattara
Ai kokarin samun warwara
Da dabarbarun kawar da asara
Jibgin jiba a jefa a shara
Mu shige shigifa
Mu samu mai mu shafa
Hannuwa mu tafa
Mu hana juna karfa-karfa
Sai hada karfin karafa
Tsintsiya madaurinki guda
Sai mu daina gada-gada
Balaguro a hanya mai gargada
A yasar da gardamar garada
Gargadina ya zam mazada
A bar yada kiren karairayi
Mu shiga taitayi
Mu yasar da bulayi
Mu tunkari karkaren kaikayi
A daina saurin daukar yayi
Ko a taro an sha shayi
Ai a kula da lumanar dan shayi
Kashe gobarar maishe da dukiya gawayi
Mai-duka ya kare tsautsayi
Damarmu ce ta kamun ludayi
Some-somen samuwa
Salamar sallamar sallamawa
Salalar sahalewa
Sulbin sululun sollewa
Sabulun salon sassabewa
Mui wa kawunanmu masalaha
Tsadar rayuwarmu ta zam arha
A fadin kasar kowace jiha
Sai ka ji dararaku hahaha
Ana ta raha