✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekaru 100: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Zarce Sa’a —Gwamnonin Arewa

A tsawon rayuwar malamin, ya kasance ginshiƙi kuma abun koyi ga al'umma

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya fitaccen malamin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi murnar cika shekaru 100 da haihuwa.

Gwamnan ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban jigo a duniyar Musulunci, wanda ya shahara da zurfin ilimin Alkur’ani, Hadisi, Fiqhu, da kuma fahimta mai zurfi a bangarorin ruhaniya na sufanci wanda ya bambanta shi a matsayin jagorar ruhaniya dai dai gwargwado.

A cewarsa koyarwar Sheikh Dahiru Bauchi ta wuce tsararraki, inda ta wadatar da rayuwar mutane marasa adadi ta hanyar tafsirin Alkur’ani mai girma.

A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mai magana da yawun gwamnan, Isma’ila Uba Misilli, ya ce a tsawon rayuwar malamin, ya kasance ginshiƙi kuma abun koyi ga al’umma.

Inuwa Yahaya, ya kuma ya bawa malamin bisa jajircewarsa wajen raya kyawawan dabi’u da ruhi, wanda ya ce sun taimaka matuka wajen inganta imanin mabiyansa da zuriyarsa, baya ga gudumawarsa wajen samar da hadin kai da zaman lafiya.

Daga nan sai Gwamna Inuwa Yahaya ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ci gaba da bai wa malamin addinin lafiya da tsawon rai don ci gaba da jagorantar al’umma.