✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekarau zai koma PDP ranar Lahadi

Mun amince za mu yi masa biyayya kuma da Yardar Allah za mu yi nasara.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai ziyarci Jihar Kano a ranar Lahadi domin karbar tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau da zai sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Ziyarar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar na zuwa ne a adaidai lokacin da ake dakon jin matsayar Sanata Shekarau da tun a makon da ya gabata ake jita-jitar tsamin dangartaka da za ta shi ficewa daga jam’iyyar NNPP.

A farkon wannan makon mai karewa tsohon gwamnan kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya nuna alamonin raba gari da jam’iyyar NNPP.

Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da BBC ya zargi jagoran NNPP kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Sanara Rabi’u Musa Kwankwaso da yaudararsu.

Bayanai sun ce ziyarar da Atiku zai kai Jihar Kanon na daya daga cikin shirye-shiryen ayyana sauyin shekar da Shekarau din zai yi zuwa jam’iyyar PDP a hukumance a ranar Litinin.

Duk da kasancewar Shekarau dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar NNPP, zai hakura da tikitin ya sauya sheka zuwa PDPn domin kara tumke damarar da samun goyon bayan karbuwar jam’iyyar a Arewa maso Yammacin kasar yayin Zaben 2023.

Da yake magana da Aminiya, Shugaban PDP na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi wanda ya ziyarci Shekarau a Asabar din nan, ya shaida wa wakilinmu cewa Shekarau ya amince zai sake komawa jam’iyyar ta PDP.

“Allah mun gode maka, a yanzu mun samu jagora a Kano kuma muna farin ciki.

­“Shekarau wanda shi ne mai rike da mukami na siyasa mafi girma a bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, mun amince kuma muna maraba da dawowarsa jami’iyyarmu ta PDP.

“A yanzu tuni shirye-shirye sun yi nisa na ziyarar da Atiku Abubakar zai kawo Jihar Kano a ranar Lahadi domin karbar Mallam Ibrahim Shekarau.

“Mun amince za mu yi masa biyayya kuma da Yardar Allah za mu yi nasara.

A baya dai rahotanni sun bayyana cewa, Shekarau ya yi watsi da zawarcin da Atiku ke yi masa na komawa jam’iyyar PDP, sai dai a yanzu ta tabbata cewa an kulla yarjejeniya tsakanin Sanatan da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar.

A halin da ake ciki dai jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano na fama da rikicin cikin gida, la’akari da takun sakar da ke tsakanin tsagin shugabanninta biyu – Bello Hayatu Gwarzo da kuma Shehu Wada Sagagi.