✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekarau ya sauya sheka zuwa NNPP —Abdulmini Jibrin

Honorabul Abdulmumini Jibrin ya koma NNPP ya sanar da sauya shekar ta Shekarau a safiyar Laraba.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP daga Jam’iyyar APC.

Tsohon Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Bola Tinubu, Honorabul AbdulMumin Jibrin, wanda a kwana-kwanan nan ya koma NNPP, shi ne ya sanar da sauya shekar ta Shekarau a safiyar Laraba.

“Kurunkus! Maraba da zuwa NNPP, Sanata Ibrahim Shekarau,” kamar yadda Abdulmumini Jibrin ya sanar a shafinsa na Twitter.

Daga yaba Jam’iyyar NNPP, ta sanya hoton tsohon gwamnan Kanon tare da Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, a ziyararsa ta baya-bayan nan zuwa gidan tsohon gwamnan mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

A ’yan kwanakin amma an yi ta tataburza game da batun sauya shekar Sanata Shekarau zuwa NNPP.

Kawo yanzu dai bai sanar da sauya shekar tasa ba, duk da cewa bangarensa da na Kwankwaso na ta tattaunawa a kan batun.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a nasa bangaren, yana kokarin hana Sanatan mai ci sauya sheka, inda ko a baya-baya nan ya kai ziyara gidan tsohon gwamnan.