✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekarar Musulunci ta 1440 BH: Fiffikon aiki da Kalandar Musulunci a kan ta Nasara

Godiya ta tabbata ga Allah Mamallaki, Mai yawan halittawa. Shi ne Wanda Ya sanya rana ta kasance haske, kuma Ya sanya wata ya kasance annuri,…

Godiya ta tabbata ga Allah Mamallaki, Mai yawan halittawa. Shi ne Wanda Ya sanya rana ta kasance haske, kuma Ya sanya wata ya kasance annuri, kuma Ya kaddara shi (watan) manziloli domin mu san kididdigar shekaru da kuma lissafi. Allah bai hallici wannan abu ba, face da gaskiya, Yana rarrabe ayoyi domin mutanen da ke sanin hikimarSa game da halitta. Ya Allah Ka yi salati da sallama ga mafificin halittarKa, Annabi Muhammad (SAW), wanda a kan hijirarsa ce aka jingina Kalandar Musulunci. Tsira da Amincin Allah su tabbata a   gare shi da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, ya ku ’yan uwa na imani! Sanannen abu ne gare ku cewa Musulunci addini ne da ya hade komai da komai na rayuwa, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Ka ce lallai ne sallata da baikona da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai” (An’am:162).

Don haka, Musulunci imani ne da kuma aiki – kama daga ayyukan wajibai (tilas) da wasunsu; kamar yadda yake mu’amala ne, kuma kyawawan dabi’u ne.

Hakika Allah Ya farlanta mana wasu ayyuka na farilla, kuma Ya danganta su da lokuta ayyanannu. Kai, mafi yawan shika-shikan Musulunci sun dogara ne ga lokaci! Ka ga dai Sallah da Zakka da Azumi da Hajji duk sun dogara ne ga lokaci. Game da Sallah, Allah Ta’ala Ya ce: “Lallai ne Sallah ta kasance a kan muminai, farilla mai kayyadaddun lokuta.” (Nisa’i: 103).

Sa’annan, cikar shekara sharadi ne wajen fitar da Zakkar kudi da ta dabbobi. Azumi kuwa Allah Ya farlanta shi a watan Ramalana ne kawai, shekara-shekara. Watan Ramalana kuwa wani yanki ne sananne na shekara. Game da Hajji kuwa Allah cewa Ya yi: “Hajji watanni ne sanannu…” (Bakara:197). Kun ga dai duk maganar ta lokaci ce!

Bayan haka, akwai wasu ibadoji ko mu’amaloli ko hukunce-hukunce a Musulunci wadanda su ma sun ratayu ne da lokuta. Misali shi ne: Iddoji (na saki ko na takaba), tsawon lokacin shayar da yaro mama ko lokacin yaye shi da maganar ila’i da zihari da hukunce-hukuncen wanda iyalinsa suka kasa jin duriyarsa da kaffarori da wasunsu. To, kun ga duk wadannan mas’alolin, hukunce- hukuncensu sun dogara ne da lokaci – wato ko a ce “wata kaza,” ko “kwana kaza,” ko “shekara kaza” da makamantan haka!

To kuma fa, a lura! Duk maganar lokacin nan da ake yi, ana nufin lokacin da shari’a ta iyakance, ta san da zamansa, ba na Kalandar Nasara ba (Girgoriyya ko ta ’yan albashi) wadda muka fi sabawa da ita. Don haka, idan watanni ne, ana nufin watannin da Allah Ya san da zamansu, wato na Kalandar Musulunci, masu farawa da Muharram su kare da Zul-Hajji,  kamar yadda Ya ce: “Lallai ne kidayar watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin Littafin Allah, a Ranar da Ya hallici sammai da kasa; daga cikinsu akwai hudu masu alfarma…” (Tauba:36). Ni dai a dan karamin karatuna, ban ga malamin da ya fassara wadannan watanni da wannan ayar take magana a kai ba, face watannin kidayar Musulunci ta Hijira! Allah Ya sa mu dace!

Don haka, ’yan uwa a lura; tun farko, akwai bambanci a tsakanin kiyasin Shari’ar Musulunci da ta Turawa ga wasu abubuwa ko lokuta. Misali a nan shi ne tsawon “kwana” (wato dare da wuni) da adadin kwanakin watanni da adadin kwanakin shekara. Domin, a Musulunci, wata yana kwana 29 ko 30; a wurin Turawa kuwa daga kwana 28 ne zuwa 31. A Kalandar Musulunci, shekara tana da kwana 354 ne ko 355; ta Turawa kuwa kwana 365 ko 366. Kun ga dai bambancin a bayyane yake! Na san wani zai iya cewa, “To ai bambancin bai da yawa.” To, sai mu ce, ai duk lokacin da aka kauce wa shari’a, to, akwai illoli masu yawan gaske! Allah Ya kiyashe mu.

Kuma ku lura ’yan uwa, ba ga mikdarin kwanakin wata ko shekara ne kawai akan samu sabani tsakanin na Musulunci da na Turawa ko wasu mutane ba, a’a, akwai wasu ma’aunai da dama. Amma abin da yake wajibi a kanmu shi ne mu san na shari’ar, mu kiyaye shi a matsayin asali, wanda duk ba shi ba kuwa a matsayin abin kimantawa ne ga na asalin. Misalan da zan iya kawowa a nan su ne:

Ma’aunin karancin Zakkar kudi (Nisabi), wato Dinari 20 ko Dirahami 200. Kun ga a nan, Dinarin shi ne asali; iyaka dai mutanen kowace kasa za su kimanta shi ne da kudin kasarsu. Misli, a nan Najeriya, sai mu kiyasta da matsayi ko darajar Naira na kowane lokaci. Shi ya sa abin yake da hawa da gangara. Masana harkokin kudi sun fi kowa sanin wannan.

Ma’aunin tsawon nisan tafiyar da za a iya soma yin kasaru a wasu mazhabobi; wato Burudi 4 ko Farsakhi 16, wanda a halin yanzu muke kiyasta shi da kilomita 83. Kun ga, a iya fahimtarmu, abin da aka ambata a harshen shari’a shi ne asali, waninsa kuwa ya kasance kiyasi. Kuma, ina ganin, ba ya dacewa mu fita batun asali, mu manta da shi, mu ce mu rike kiyasi kawai. To, gobe idan aka canja wannan ma’aunin kiyasin fa zuwa wani? Tunda yanzu haka, wadansu sun yi ta kai bukatocinsu (ga Majalisar dinkin Duniya) na a canja wannan kalanda ta Turawa (ta Girgoriyya) daga wata 12 zuwa wata 13! (Dubi bayanin kundin sani na “Microsoft Encarta, 2009” a karkashin maganar “Kalanda”). To, misali, idan haka ta faru, yaya ke nan? Ishara dai ta isa ga mai hankali!

 

Muhimmancin amfani da Kalandar Musulunci:

Amfani da Kalandar Musulunci yana da muhimmanci kwarai-musamman ga Musulmi, ta fuskoki da dama; kuma ga kadan daga ciki:

Kalandar Hijira an aza ta ce a kan imani da Allah da kiyaye Sunnar Annabinmu Muhammad (SAW) da kiyaye Tarihin Musulunci da kuma bayyanar da wadatuwarsa da kansa a komai, hatta a sha’anin kididdigar watanni (kalanda). A daya bangaren kuma ta Girgoriyya (AD/CE/G) ma’anar sunanta na “A.D” (Anno Domini = in the year of our lord) tana nuni zuwa ga shirka da Allah Ta’ala, (Dama-dama ma a lakaba mata C.E (Christian Era) ko G = Gregorian).

Sunayen watanninmu suna da alaka da imaninmu da ibadojinmu: Muharram…Rabi’ul Awwal…Ramadan…Zul-Hajji, a lokacin da nasu suka samo asalinsu mafi yawa ko daga gunki, ko wasu kafirai. Misali: ‘January’ daga gunkin Janus, ‘February’ daga gunkin Februs ‘August’ daga Augustus Caeser.

Kiyaye ibadoji wajibai (farilla) irin su Azumi (Ramadan), Zakka (shekara-shekara) da Hajji.

 Ribatar kwanaki masu falala; irin su: 10 na farkon Zul-Hajji da Ranar Arfa da Tasu’a da Ashura da Nisfu Sha’aban da sauransu.

Sha’anin haila da idda da sauransu ya fi dacewa da kalandar Hijira.

A kimiyance, amfani da Kalandar Kwanakin Wata (Lunar Calendar) irin ta Hijira ya fi dacewa da duniyar nan tamu bisa ga kalandar rana (Solar Calendar) saboda dalillai kamar haka:

Wata ya fi kusa ga duniyarmu (Ard) bisa ga rana

Nisan wata daga duniyarmu: mil 238,840 (kilomita 253,170.4)

Nisan rana daga duniyarmu: mil 93,000,000 (kilomita 98,580,000)

To,  

Ke nan, nisan rana daga gare mu ya ninka na wata sau 389!

Wannan watan shi kadai ne (watan ‘satellite’) na wannan duniyar, yayin da wasu ’ya’yan rana ‘Mercury’ ‘benus’ da ‘Pluto’ ba su da shi, wasu kuma suna da – misali, duniyar ‘Uranus’ tana da watanni 5, duniyar ‘Saturn’ tana da watanni 10, duniyar ‘Jupiter’ tana da watanni 12.

Wata da duniyarmu sun fi alaka da juna ta fuskar jujjuyawa/tafiyarsu har masana abin na kiransa ‘double-planet’ (Earth-Moon system)

Ta fuskar tattalin arziki; ai kashe miliyan 354 ko miliyan 355 a shekara, ya fi a ce an kashe miliyan 365!

(Daga Littafin Farfesa Hussaini Akande Abdul-Karim “The Significance of Hijrah Calendar System to Mankind”).

A takaice dai, nasiharmu a nan ita ce mu yi kokari mu rika amfani da Kalandar Musulunci a dukan ibadoji ko mu’amalolinmu masu bukatar haka iyakar iyawarmu, musamman abubuwanmu na karan-kanmu, wadanda ba na hukuma ba, irin su shata ranakun daurin aure da sauran bukukuwanmu, ko na kungiyoyinmu wadanda ba na gwamnati ba. Amma abin da ya shafi hukuma, wanda ba mu da iko a kansa, sai mu tafi da shi haka nan, gwargwadon yadda yake yiyuwa, a kan lalura, tare da yin aiki (kokarin kawo gyara) da kuma fatar ganin cewa komai tsawon dare gari zai waye insha Allahu!

Allah Ya taimake mu, Ya sa mu dace.

Wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE), Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi za a iya samunsa ta: +2348036049452, 08181059714, Imel: ([email protected]).