✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekara 25 bayan gwajin rigakafin Pfizer a Kano, har yanzu tsugune ba ta kare ba

A lokacin yara sama da 200 ne aka yi wa riga-kafin a Asibitin Zana, inda da dama daga cikinsu suka rasu.

A 1996, kimanin shekara 25 da suka gabata ce, hamshakin kamfanin harhada magunguna a kasar Amurka mai suna Pfizer ya ziyarci Jihar Kano da nufin bayar da maganin cutar sankarau, amma lamarin ya zo da matsala, bayan da aka zargi kamfanin da yi gwajin maganin a kan mutane.

A lokacin yara sama da 200 ne aka yi wa riga-kafin a Asibitin Zana, inda da dama daga cikinsu suka rasu, wadansu suka samu nakasa kamar kurumcewa ko makancewa, yayin da wadansu da dama suka gamu da larurar tabin hankali ko fama da nau’o’in nakasa iri-iri.

Bayan kai-ruwa-rana na tsawon shekaru, a karshe an cimma matsaya, inda kamfanin ya amince ya biya iyalan yara diyya, a karkashin wata kungiya da Mustapha Maiskeli yake jagoranta.

Har yanzu akwai sauran rina a kaba

To sai dai duk da wannan fafutika, har yanzu akwai wadansu daga cikin iyalan yaran da wannan matsala ta shafa da har yanzu suke korafin ba a biya su hakkokinsu ba.

A zantawarsa da Aminiya, Muhammad Auwalu Inuwa, Shugaban Kungiyar da ke Fafutikar Neman Hakkin ’Yan uwansu daga Kamfanin Pfizer ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba a fafutikar tasu.

“Daga bangarenmu, an zo an yi wani irin biya an ba su mafi karancin, kamar yadda suka kira shi da tallafi. Domin shi kansa kamfanin bayan ya yi wannan allurar da ta mayar da wadansu kurame, wadansu makafi, wadansu kuma suka mutu, wadansu suna nan a raye amma ba su da wata moriya da ya san cewa ya yi mana illa sai ya amince zai biya diyya.

Day daga cikin wanda rigakafin ta nakasta

“Bayan sun yi wannan allura ta zalunci sannan suka ce za su biya. Daga farko sun fara biyan diyyar Dala 175,000 ga kowa da kowa, amma daga baya sai abu ya canja bayan wadansu sun tayar da tarnaki, aka rasa gane ma a ina aka kwana.

“Sannan lokaci guda Pfizer ya ce an cimma yarjejeniya a wajen kotu zai biya kowa kudi na baixaya. Mun yi ta sauraro mu ga ta yaya za a biya, shin za a ci gaba da wancan adadi na Dala 175,000 ne? Amma kawai sai muka ji cewa mu vangarenmu an ba mu Dala 7,000, wani bangaren kuma a can an ba su har Dala 25,000,” inji shi.

‘A biya mu kamar yadda aka biya sauran’

Shugaban ya qara da cewa yanzu abin da suke fafutika a kai shi ne bai wuce kira ga masu ruwa-da-tsaki su shigo su ga cewa an yi adalci da daidaito ba.

Wata daga cikin wadanda riga-kafin ta illata

“Bai kamata a ba wadansu mafi yawan kudi, wadansu kuma a ba su mafi karanci ba. Mene ne ya bambanta su? Shekara daya aka yi wannan gwajin, a asibiti daya kuma kamfani daya ne ya yi, mene ne na bambanta biyan?

“Muna nan muna bibiyar wannan hakkin namu kuma duk inda ya kama za mu shiga don ganin an mana adalci.

“A cikin yaran nan fa wadansu sun kurumce, wadansu sun makance, wadansu sun samu tabin hankali. Akwai waxanda kana cikin magana da su kawai sai ka ga sun saki fitsari. Wadansu kuma ma mata ne har yanzu suna nan sun kasa samun mazan aure saboda wadannan nau’o’in nakasa,” inji shi.

‘Dana har yanzu ba ya iya yin komai’

Alhaji Kasimu Jibrin Kofar Waika, wani mahaifi da gwajin ya yi wa dansa illa, ya ce yanzu haka dansa ba ya iya daukar komai da hannunsa, sannan kafarsa ta lankwashe.

Ya ce, “Kunnuwansa na bari daya in kana masa magana ba ya jin ka. Sannan wani lokacin kana yi masa magana za ka gane cewa kwakwalwarsa ba lafiya take ba.

“Lokacin da aka kai shi Asibitin Zana a wancan lokaci ba ya da lafiya ne, an kai shi ne a yi masa riga-kafin sankarau kawai sai suka yi masa wannan allura.

“Maganar kudi kuma Dala 7,000 aka ba shi,” inji mahaifin.

Daga nan sai ya yi kira ga masu ruwa-da-tsaki su sa baki a maganar don ganin an yi adalci wajen biyansu kamar yadda aka biya ragowar mutanen.

‘Ainihin abin da ya faru’

Aminiya ta tuntuvi Alhaji Bello Muhammad, wanda shi ne ya rika shiga tsakani, ya ce shi kansa lamarin ya jefa shi a tsaka-maiwuya.

A cewarsa, “Mun jima muna wannan fafutika a daidaikunmu, amma zamanin mulkin Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sanya baki a ciki, bayan wata kungiya da Maisikeli yake jagoranta sun kai Pfizer kara a kotu.

“To kasancewar mu ma muna cikin wadannan mutane amma ba mu shiga cikin waccan kungiya ba lokacin da aka shigar da karar, sai muka amince mu kafa tamu kungiyar bayan ta Maisikelin, inda yawanmu ya kai 347.

“Daga karshe dai aka amince ta hanyar yin yarjejeniya a wajen kotu cewa kamfanin zai biya ’yan kungiyar Maisikeli wadanda suka kai waccan karar Dala 25,000, mu kuma da muka zo daga baya aka ce za a ba mu Dala 10,000 kowannenmu.

“To inda aka samu matsalar shi ne bayan tantance mu, sai da aka dauki sama da shekara biyu kafin kudin su fito, a hakan ma kuma sai aka ba mu Dala 7,000 maimakon Dala 10,000 da aka yi alkawari tun da farko.

“Wannan ne ya jawo zarge-zarge iri-iri, har ma wadansu ke zargin cewa masu biyan kudin ne suka zabtare musu, shi ne dalilin da ya sa suke korafi kan waccan cikon Dala 3,000,” inji shi.

A ina gizo yake saqar?

Mun yi yunkurin jin ta bakin bangarorin Maisikeli da na wakilan Kamfanin Pfizer, sai dai yunkurin namu ya ci tura saboda bangarorin biyu sun ki cewa uffan kan lamarin. Sai dai wata majiya mai tushe wacce ba ta amince a ambaci sunanta ba, ta musanta zarge-zargen, inda ta ce ba su da tushe ballantana makama.

A cewar majiyar, suna kokarin kawo ruxani ne kawai a batun, kasancewar Kamfanin Pfizer ya riga ya gama sallamarsu gaba daya.

To sai dai wata majiyar ta daban ta shaida wa Aminiya cewa kamfanin ne ya ja kunnensu da kada su kuskura su qara cewa wani abu a kai. Kazalika,Aminiya ta gano cewa ofishin Kamfanin Pfizer na Kano ya tashi ya koma Legas inda ya canja sunansa zuwa wani daban saboda gudun ci gaba da cece-kuce.

Duk kokarin Aminiya na jin ta bakin lauyan Kamfanin Pfizer, Nelson Nzeogwu ya ci tura.

Wakilinmu ya yi ta kiran wayarsa da farko amma ya ki dagawa, ya aike masa da sako shi ma bai dawo da amsa ba kusan mako guda.

Daga baya ya daga wayar bayan sake kiransa amma sai ya ce lambar ba daidai ba ce.

Wannan sa-toka-sa-katsin da Kamfanin Pfizer na ci gaba da yamutsa hazo ne a daidai lokacin da kamfanin ya samo tare da sarrafa allurar riga-kafin COVID19 a duniya, lamarin da wadanda wancan gwajin na baya ya shafa suka ce suna dari-dari da shi.