Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, kuma daya daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 100 cif da haihuwa, a ranar Litinin da ta gabata 2 ga Muharram 1446 Bayan Hijira, a kidayar shekarar Musulunci.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda babban jigo a Darikar Tijjaniyya a Nijeriya da Afirka, shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya.
- An kafa kwamitin magance rikicin manoma da makiyaya a Ekiti
- Tinubu ya sauya Shugaban Hukumar Tashohin Ruwa
Duk da cewa iyalai da almajiran Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi ba su yi wani biki don taya shi murnar cika shekara 100 a duniya, amma masoya da almajiran Shehin Malamin sun bayyana farin cikinsu a dandali daban-daban na shafukan Intanet inda suka rika bayyana farin cikinsu kan wannan muhimmin abin tarihi.
Wannan lokaci ya zo ne a daidai lokacin da Farfesa Khalid Abdullahi Zariya ya shafe shekaru yana bincike kan rayuwar Shehin Malamin, inda ya rubuta littattafai uku da yake kokarin kaddamar da su kan rayuwar Shehin.
Farfesa Khalid ya ce, Shehin ya bayyana masa abubuwan da yake iya tunawa a rayuwarsa tun yana dan shekara uku a duniya.
Sai kuma Malam Auwwal Zubayr da ke Kano wanda shi kuma ya yi nazari kan rayuwar Shehin, inda ya yi tafiye-tafiye ciki da wajen kasar nan kuma ya shirya faifan bidiyo a kan rayuwar Shehin da shi ma ke kokarin kaddamarwa.
A wata zantawa da ya yi da manema labarai a shekarun baya a Bauchi, Shehu Dahiru Usman Bauchi ya ba da takaitaccen tarihinsa inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukkan kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.
“To ni dukkanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska.
“Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.
“Bayan da aka raba Bauchi da Gombe, sai muka zama Fulanin Jihar Bauchi, a lokaci guda Fulanin Jihar Gombe.
“Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.
“An haife ni a watan Janairun 1927 wanda ya yi daidai da 2 ga watan Muharram, 1346 Bayan Hijira a ranar Laraba.
“Sunan mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adamu, shi mahaddacin Alkur’ani ne. Na rayu a hannunsa shi ya koya mani karatu har na haddace Alkur’ani a hannunsa.
“Sunan mahaifiyata Hajiya Maryam. Bayan na haddace Alkur’ani a hannun mahaifina ne ya tura ni duniya domin in je in gyara tilawata ta Alkur’ani.
“ Na shiga duniyar Allah Ya taimake ni na gyara tilawar tawa, lamarin da ya sanya wasu kan ce mani Gwani na Alkur’ani, wasu mutanen kuwa kirana suke yi da Gangaran a fagen haddar Alkur’ani.
“Bayan nan sai mahaifina ya ce zai tura ni in je in sake nemo ilimi. Daga nan aka turo ni nan Bauchi domin neman ilimi.
“Na fara neman ilimi ban riga na samu ilimin da yawa ba, sai Allah Ya sa Failar Shehu Ibrahim Kaulaha ta bayyana.
“Dama mahaifina dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne ta salsalar Umarul Futi, wato ta wajen Muhammadu Ghali. Kuma shi mahaifina ne ya ba ni Darikar Tijjaniyya.
“Bayan da muka shiga Failar Shehu Ibrahim, sai ya zama kowace harka tawa sai ta hada da maganar Shehu Ibrahim.
“Alhamdulillahi na samu rabo mai tarin yawa a sha’aninsa, na soma yin tafsirin Alkur’ani ne da aurensa na farko a 1948.
“Cikin alherin da Allah Ya yi mini, ’ya’yana tun suna kanana suke haddace Alkur’ani.
“Da farko ’ya’yana suna haddace Alkur’ani tun suna ’yan shekara 11, aka dawo 10, aka zo 9 har ya zamana cewa akwai ’ya’yana da suka haddace Kur’ani suna ’yan shekara bakwai-bakwai da haihuwa,” in ji Shehin.
Ya ce, “Abin da ya fi ba ni sha’awa a rayuwata shi ne yadda na mayar da Alkur’ani sana’ata da kuma yadda na rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwata, kuma da duk wani mutumin da yake dangantuwa da son Annabi (SAW) da son Allah ina sha’awar in hadu da shi.
“A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karatun Alkur’ani da karanta Salatul Fatihi da Tasbihi da Istigfari da Salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori.”
Da aka tambaye shi kan mutane na mamakin dimbin ilimin da Allah Ya ba shi kuma ko akwai fannin da ya fi kwarewa?
Sai ya ce “Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Kur’ani, kuma ta hannunsa ne na karbi Darikar Tijjaniya.
“Shi mahaifina ya karbi Darikar Tijjaniya ce ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba.
“Daga baya sai mahaifina ya ba ni izinin ia tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Alkur’ani Mai girma.
“Bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkur’ani. Daga nan sai bangaren Tafsiri, a nan malaman Tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri, inji su.
“Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa ita ce ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiransa ilimin tarbiyya. A nan ma masu irin ilimi kan ce ina da sani a fannin.
“Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare. Sauran ilimomi ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu duk ina tattabawa,” in ji shi.
Da aka sake tambayarsa cewa jama’a na mamaki idan aka yi wa Malam fatawa sai ya hada da ba da misali maimakon gundarin amsar, ko me ya sa yake yin haka?
Sai ya ce, “Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane, idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su.
“Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci me aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa.”
Shehin Malamin masanin Tafsirin Alkur’ani Mai girma ya samu lambobin yabo a wannan bangare, ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori dabandaban a Nijeriya da sassan duniya.
Jami’ar Tarayya da ke garin Lafiya a Jihar Nasarawa ta karrama shi da digirin girmamawa na Dokta, kuma Gwamnatin Tarayya ta ba shi Lambar Girmamawa ta Kasa ta OFR.
Kadan daga cikin nasarorin da Sheikh Dahiru Bauchi ya samu a rayuwarsa
Sheikh Dahiru Bauchi ya musuluntar da dubban mutane. Ya kuma bai wa dubban mutane Wuridin Darikar Tijjaniyya.
Shehi a duk lokaci bayan lokaci yana karanta Alkur’ani kuma yakan yi saukar Alkur’ani a kwana biyu.
Sama da mutum dubu 200 da 924 suka haddace Alkur’ani Mai girma a makarantunsa da ke fadin Nijeriya.
Shehun Malamin ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,600 a Nijeriya da Afirka.
A karkashin gidauniyarsa an gina azuzuwan karatu dubu 153 da 80 a Arewacin Nijeriya.
Shehi, mutum ne mai kishin kasarsa mai son Nijeriya, kuma mai kaunar zama lafiya wanda a duk lokacin da ya bude baki zai yi addu’a sai ya roki Allah Ya ba da lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.
A cikin littafin tarihin rayuwar Shehin mai “Suna Shehu Dahiru Bauchi: Ginin Allah,” Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, ya ce, ’ya’yan da Shehu ya haifa a duniya su 100 ne; mata 48, maza 47, Mahaddata Alkur’ani daga ciki su 77 ne.
Daga cikin ’ya’yansa 13 sun rasu, saura 82. Sannan ya ce an gano cewa Shehin ya haifi wasu yara biyar wadanda tun ba a yi radin sunansu ba suka rasu, jimilla 100 ke nan.
Farfesa Khalid wanda ya rubuta littafai uku masu shafi 1,111 kan rayuwar Shehin ya ce “Allah ne Ya yi riko da hannuna na rubuta littattafan da nufin bayyana alheran da rayuwar shekara 100 masu albarka cikin Musulunci da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ke ci gaba da gudanarwa.
“Za su taimaki tarihi da dalibai da masu gudanar da bincike a makarantu.”
Ya ce yana rokon Allah ya kara sanar da al’ummar duniya wane ne Maulana Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi?
Shehi ya yi shekara 75 yana Tafsirin Alkur’ani, tun 1948 shekara 12 kafin Nijeriya ta samu ’yancin kai, kuma Shehin ya haifi ’ya’ya da jikoki fiye 400 mahaddata Kur’ani.
Yana da zuriyar da suka fito daga jikinsa da suka kai mutum 1,000.
Shehu Ɗahiru ne almajirin Kur’ani da ya fi daɗewa da barin gidansu don neman ilimi.
Bayan haddacewa da rubutawa da hannu da ya yi a tsangayar mahaifinsa Alhaji Usman, tun 1947 mahaifinsa ya ce ya koma Bauchi daga garinsu Konkiyel da ke Karamar Hukumar Darazo, kuma har yau bai koma ba.
Ya ce “Allah Ka kara duba bawanKa Shehu Ɗahiru Bauchi wanda ’ya’yansa 77 suka haddace Kur’ani. Jikoki zuwa ’ya’yan jikoki 313 mahaddata.
“Shehu Ɗahiru Bauchi ne ya fara gudanar da Tafsirin Kur’ani ba tare da dubawa ba, musamman a tarihin Tafsiri a Afirka, kuma shi ne Bafulatanin da yake yin Tafsiri da karbabbiyar Hausa da akasarin mutane suke iya fahimta.
“Tsohon Shugaban Kungiyar Daliban Makarantun Sheikh Dahiru Bauchi, Malam Ibrahim Imam Isma’ila ya ce a tarihi ban da Maulana Sheikh Dahiru Bauchi, babu wanda ya taba yin arzikin ’ya’ya da jikoki da ’ya’yan jikoki mahaddata wajen 400.
“Muna rokon Allah Ya kara inganta lafiyarsa, Ya tsawaita rayuwarsa cikin aminci da natsuwa,” in ji shi.
Almajiran Shehin, Sarki Alhaji Sanusi Ahmad da Malam Ahmad Tijjani Kolo da Malam Muhammad Jibril Sogiji, sun ce Shehi ya samu nasara matuka wajen hada kan al’umma, idan aka yi la’akari da manyan tarurrrukan Musulunci biyar da yake yi kowace shekara a Nijeriya.
Kamar lokacin farawa da rufe Tafsirin Alkur’ani kowace shekara da lokacin yin Maulidin Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) da Maulidin Shehu Tijjani da Maulidin Shehu Ibrahim Nyass da kuma taron Zikirin Juma’a na farkon shekarar Musullunci a Muharram.
Almajiran sun ce cikar Shehi shekara 100 ta zo da albarka, domin a wannan lokaci ne aka gina wa Shehin katafaren masallaci da makaranta da dakin taro wanda shi ne irinsa na biyu a duk fadin Afirka.
Kuma a wannan lokaci ne aka samu dalibai a hannun Shehin su 100 da suka haddace Alkur’ani da dukkan kira’o’i sannan da aka ruwaito ake yin kira’a da su sabanin yadda a baya sai dai ka haddace da kira’ar Warshu ko Hafsu.
Wani almajirin Shehin, Tsohon Shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi,
Malam Ahmad Tijjani Sa’id ya ce rayuwar Shehi gaba daya makaranta ce, ta raya ilimi da tarbiyyantar da al’umma, saboda a yau a raye, shi ne cikin malamai wanda za ka samu ya yi tafiya daga Potiskum zuwa Filato a kafa don yada addinin Musulunci.
“Ya yi tafiya daga Arewa zuwa Kudu a kan jaki da doki don yada addinin Musulunci.
“Ya yi tafiya a kan keke zuwa kauyuka da dama kamar Tafawa Balewa yankin Gindiri da Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma don yada addinin Musulunci.
“Haka lokacin da mota ta zo Shehi bai huta ba har lokacin da jirgin sama ya zo, duk da tsufarsa yana yawon gwagwarmayar yada Musulunci da darika har zuwa yanzu ga tsufa amma zuciyarsa ba ta gaji ba, shi ya sa ba za ka samu wanda yake iya yin himma irin tasa ba,” in ji shi.
Uwargidansa Hajiya Safiyya Sheikh Dahiru ta ce babban abin mamaki a wurin Shehi, “Shi ne ba ya fushi sai dai mu da kanmu mu gane mun yi masa laifi, mun yi masa ba daidai ba, mu ba shi hakuri.”
Daya daga cikin hadimansa Abubakar Ibrahim ya ce, “Alhamdulillahi, Allah cikin IkonSa yau 2 ga watan Muharam 1446 Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 100 a duniya.
“Hakika babban abin da ya daukaka Shehu shi ne Alkur’ani. A tarihin duniya ba a taba samun wani malami da Allah Ya sahale wa Kur’ani irin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba, domin sai mu ce bayan zuriyarsa makwabtaka ka yi da Shehu sai ’ya’yanka sun haddace Kur’ani in dai ka mika su gare shi.
“Shehu ya zama ko makiyinsa ne sai dai su yi suka ko zagi amma sun san da wannan. Ko Kiristocin Nijeriya sun san babu malamin Musulunci irin Shehu a Nijeriya saboda su kansu shaida ne ya musuluntar da kakaninsu da yawa,” in ji shi.
Ya ce, “Ayyukan Shehu ga Musulunci ba sa kirguwa. Shi ne malamin na farko a tarihin duniya da ya shekara 75 yana tafsirin Alkur’ani da harsunan da suka fi karfi a Afirka wato Hausa da Fulatanci.
“Allah Ya kara wa Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi lafiya da nisan kwana alfarmar Ma’aiki (SAW).