Shahararren malamin Musulunci kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya cika shekaru 100 a duniya a kalandar Musulunci.
An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar 2 ga watan Almuharram shekara ta 1346 bayan hijira.
A ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2024, fitaccen malamin ya ci a shekara 100 a bisa lissafin kalandar Musulunci.
Sheikh Dahiru Bauchi ya tafiyar da rayuwarsa wajen bayar da gudunmawa a fannin ilmin addinin Musulunci.
An haifi Sheikh Dahiru Bauchi a garin Nafada a tsohuwar Jihar Bauchi amma yanzu yana karkashin jihar Gombe.
Tarihin Sheikh Dahiru Bauchi
A halin yanzu Sheikh Bauchi yana zaune ne a Kofar Gombe.
Karatunsa
Ya fara karatunsa na Musulunci ne a hannun mahaifinsa, Alhaji Usman, inda ya haddacce Alkur’ani mai girma tun kafin ya cika shekara 20 a duniya.
Ya ci gaba da karatunsa a karkashin manya malaman Musulunci na ciki da wajen Najeriya, inda Sheikh Ibrahim Inyass ya kasance babban malaminsa.
Zurfin ilimin Sheikh Dahiru Bauchi
Zurfin iliminsa ya kai ga karrama shi a matsayin Gangaran a fannin haddar Alkur’ani da sauran fannoni.
An kuma karrama shi a matsayin daya daga cikin manyan masana tafsirin Alkur’ani Mai Girma a duniya.
Tafsirin Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Bauchi ya fara Tafsirinsa ne a Jihar Bauchi a shekarar 1948, kuma ya shafe shekaru 76 wajen yin tafsirin Alkur’ani mai girma.
An fara yada Tafsirinsa a gidan rediyon Bauchi a shekarar 1976, kafin daga baya gidan rediyon Najeriya Kaduna ya fara yadawa a 1980.
A halin yanzu, gidajen rediyo da dama a arewacin Najeriya suna yada koyarwarsa, musamman a cikin watan Ramadan.
Uban mahaddata Alkur’ani
Babban malamin na da ’ya’ya kimanin 100 da jikoki 406, da tattaba-kunne jikoki 100, wadanda su ma suka gaje shi a fannin haddar Al-Qur’ani.
Abin sha’awa, 78 daga cikin ’ya’yansa da jikoki sama da 199, da tattaba kunne 12 su ma sun haddacce Al-Kur’ani, hadi da ilimin boko da na addinin Musulunci.
Sheikh Bauchi ya yi aikin Hajji sau 55 da Umrah sau 205.
Taimakon Al’umma
Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma samar da gidaje kimanin 1,000 a jihohin Bauchi da Kaduna, da sauran jihohin Arewa, domin ’ya’yansa da almajiransa su zauna kyauta.
Ya kuma kafa makarantun Islamiyya da noma da dama.
Sheikh Bauchi ya shahara da hikimar yin wa’azi, wanda ya sa mutane da dama suka Musulunta, musamman a watan Ramadan.
Malamin na yawan kira ga Allah Shi kadai, da yawaita istigfari da hailala hamdala da yin salati ga Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Mukaminsa
Shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya.
Duk da cewa ba a yi bikin cika shekaru 100 da haihuwa ba, almajiransa da malamai sun gudanar da addu’o’i na musamman a masallatai, tare da nuna godiya bisa gudunmawar rayuwarsu da nasarorin da ya samu.
Sun yaba da irin hidimar da ya yi wa Musulunci da Bil Adama, inda suka jinjina rawar da ya taka a matsayinsa na shugaba mai kishi da kuma tsayuwar daka.
Daya daga cikin almajiransa, Malam Ahmad Tijjani Saeed ya ce, “Yayin da Maulana Sheikh yake cika shekaru 100 cikin koshin lafiya, ya bar abin koyi mai tarin yawa a rayuwa wajen bauta wa bautar Allah da hidimta wa al’ummarsa da kuma bil’adama.”
Sauran almajiran irinsu Malam Ahmad Tijjani Kolo, Sanusi Ahmad, da Muhammad Sogiji, sun yaba wa jajircewar Sheikh Bauchi wajen yin magana kan azzalumai, da cin hanci da rashawa, da kuma matsalolin zamantakewa kamar rashawa, kungiyoyin asiri, da shaye-shayen miyagun kwayoyi.