✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi

Ya ce yana samun sassan daga sabbin kaburbura, waɗanda hatsari ya rutsa da su

Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya kai kimnanin shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi.

Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun.

A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga.

“Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka watsar a gefen hanyoyi,” in ji shi.

Wanda ake zargin, wanda ya amsa laifinsa ga wani taron jama’a da suka yi yunƙurin kashe shi kafin sojoji su cece shi, ana zargin yana kan hanyarsa ne na kai wani sassan jiki ga wani mai siye lokacin da aka kama shi.

Daga nan aka miƙa wanda ake zargin ga ’yan sanda a yankin Noforija don ƙarin bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

Laftanar Kanar Olabisi Olalekan Ayeni, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 81, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayan kama wanda ake zargin daga baya an miƙa shi tare da kayayyakin da aka samu a wurinsa, ga ’yan sandan Najeriya don ƙarin bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

“Sojojin sun ceto wanda ake zargin daga wani taron jama’a da suka yi yunƙurin kashe shi,” in ji shi.