A ranar Talata 19 ga watan Fabrairun 2019 ne Leah Sharibu, daliba a Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnati da ke Dapchi a Jihar Yobe ta cika shekara guda cur a hannun ’yan kungiyar Boko Haram.
A ranar 19 ga Fabrairun bara ne kungiyar ta yi dirar mikiya a Kwalejin Sana’a da Kimiyya ta ’Yan mata ta Gwamnati (GGSTS) da ke Dapchi a Jihar Yobe ta yi awon gaba da ’yan mata 110 ciki har da Leah Sharibu.
Rahotanni sun nuna tuni kungiyar ta saki sauran ’yan matan amma ta ki sakin Leah Sharibu. An ce kungiyar ta ki sakin Sharibu ce saboda ta ki yarda ta koma Musulma daga addininta na Kirista.
Kafin kungiyar ta kai hari makarantar Dapchi, ta taba kai samame a Kwalejin Gwamnati ta ’Yan mata da ke garin Chibok da ke Jihar Borno inda ta yi awon gaba da fiye da ’yan mata 200. Duk da tuni ta saki wadansu, har yanzu wadansu ’yan matan suna tsare a hannunsu kuma ba a san halin da suke ciki ba.
Sai dai garkuwar da kungiyar ta yi da Leah Sharibu ya fi jan hankalin duniya, ganin yadda abin ya shafi addini, kuma matashiya ce ’yar kimanin shekara 16 a lokacin da abin ya faru, inda yanzu za a iya cewa ta kai shekara 17 bayan ta shafe shekara 1 a hannunsu.
A yayin da ake kamfe kafin zaben bana, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo sun nuna damuwarsu game da rashin sako Leah Sharibu. Osinbajo a wata ziyara da ya kai ga iyalan Leah Sharibu ya nanata kudirin Gwamnatin Tarayya na ganin an sako ta cikin gaggawa ba tare da an samu wata matsala ba. A lokacin, Osinbajo ya sha alwashin ganin Gwamnatin Tarayya ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sako budurwar.
Shi ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a watan Oktoba ya yi magana da iyalan Leah Sharibu ta waya kai-tsaye, inda ya ba su hakuri kuma ya tabbatar musu kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na ganin an sako Leah Sharibu ba tare da ko kwarzane ba.
Kafofin watsa labarai ciki har da kafofin sadarwa na zamani sun yi ta yayata kiran da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ga iyalan Leah don a nuna yadda ya damu da al’amarin.
A nasa bangaren Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Osinbajo ya tabbatar wa iyalan Sharibu kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na ganin Boko Haram ta sako musu ’yarsu. Ya ce gwamnati za ta yi amfani da dillalai ne da ake ganin suna hulda da kungiyar don ganin an yi yarjejeniyar sako Leah.
Sai dai ga iyalan Leah Sharibu sun dauki wannan alkawari tamkar tatsuniya, don sun sha jin irin wadannan kalamai daga bakuna daban-daban da suka hada da jami’an tsaro da bangaren gwamnati da kuma a daidaikun mutane amma har yanzu shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Yau shekara guda ke nan da ake yi musu alkawura daban-daban game da sako Leah Sharibu amma shiru kake ji wanda hakan ya ci gaba da jefa su cikin zullumi da tashin hankali.
Jim kadan bayan an bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa karo na biyu da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairun bana, sai Misis Rebecca Sharibu, mahaifiyar Leah Sharibu ta aika sakon taya murna ga Shugaba Muhammadu Buhari. “Ina taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe a karo na biyu, sannan ina taya daukacin ’yan Najeriya murna kan gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da an samu wata hatsaniya ba. Sai dai ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya yi mana na sako ’yarmu Leah Sharibu da har yanzu take hannun ’yan kungiyar Boko Haram bayan shekara daya,” inji ta.
A nan, muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sako Leah Sharibu da duk wadanda suke tsare a hannun ’ya’yan kungiyar Boko Haram.
Bai dace kungiyar ta rika yin garkuwa da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, don kawai tana fada da gwamnati. Ya dace ’ya’yan kungiyar su rika bin matakan sulhu a duk lokacin da aka yi musu ba daidai ba, maimakon su rika kama ’yan kasa suna yin garkuwa da su.
Sannan babu wani addini da ya amince a tilasta wa wani ko wadansu su bi addinin da ba su so, don haka yunkurin da kungiyar ke yi na tilasta wa Leah Sharibu ta canja addini sam bai dace ba.
Muna fata kungiyar Boko Haram za ta bi matakin sulhu kuma za ta yi amfani da tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi mata na rungumar sulhu da hakan zai sa a yafe laifuffukan da suka aikata a baya ba tare da an hukunta su ba.