✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 1 da rasuwar Sheikh Ahmad Bamba

7 ga watan Janairun shekarar 2022 rana ce da hantar al'ummar Musulumi ta kada, musamman daliban ilimi a Najeriya da sauran wurare.

7 ga watan Janairun shekarar 2022 rana ce da hantar al’ummar Musulumi ta kada, musamman daliban ilimi a Najeriya da sauran wurare.

Labarin rasuwar malamin Musulunci, Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Bamba, a ranar ta girgiza su — daga mai istirja’i, sai mai hailala, sai mai zubar da hawaye, sai mai salati, sai mai yi masa addu’a.

Ba tare da bata lokaci ba, daga ko’ina a Najeriya da sauran wurare, mutane suka kama hanyar zuwa Kano domin halartar jana’izar malamin; kan ka ce kwabo, jama’a daga kusa da nesa sun yi cikar kwari a masallacin udun Yola domin samun ladar halartar jana’izarsa.

Sheikh Dokta Ahmad Bamba, wanda Allah Ya yi wa rasuwa sakamakon jinya, tsohon malami ne a Jami’ar Madina da ke Saudiyya, inda ya shafe sama da shekara 20 yana daukar darasi a Masallacin Annabi Muhammad (SAW) da ke Madina.

Sannan kuma tsohon malami ne a Jami’ar Bayero ta Kano, bayan nan ya shafe yi kimanin shekara 40 yana jagorantar majalisin ilimi a Kano kuma karatuttukansa sun bazu a duniya cikin harshen Hausa.

A majalisin nasa, ya fassara manyan litattafan Musulunci irin su, Muwadda Mali da Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunanu Abi Dawud da Sunanu Nasa’i da Sunanu Tirmizi da Sunanu Ibn Maja da Sunanu Darimi da Musnad Ahmad bn Hambal da sauransu.

Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Bamba, wanda aka fi sani da Dokta Ahmad BUK ko Ahmad Bamba, tun yana raye al’umma ke masa kyakkyawar shaida game da kyawun dabi’unsa da tsantseninsa da kuma nisantar harkokin siyasa.

Malami ne kuma ga manyan malaman Musulunci da suka yi fice a duniya, ciki har da marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam — kuma ya kasance abin koyi ga daliban ilimi da sauran mutane, a Kano da sauran wurare.

Ya fara assasa majalisinsa na Darul Hadis ne a Masallacin Juma’a da ke tsohuwar harabar Jami’ar Bayero, kafin daga baya ya koma masallacinsa da ke Tudun Yola.