✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Dokta Yusuf Ali ya rasu

Yau da Azahar za a yi jana'izar fitaccen malamin Musulunci a Kano, Sheikh Dokta Yusuf Ali, a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Shaikh Dokta Yusuf Ali rasuwa.

Sheikh Dokta Yusuf wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya ya rasu ne a daren Lahadi bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73.

Yar marigayin, Dokta Bilkisu Yusuf Ali ta shaidawa Aminiya cewa za a yi janaizarsa a yau Litinin da Azabar a Masallachin Murtala da ke kan titin Gidan Zoo.

Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alkali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban a Jihar Kano, kafin ya yi ritaya a shekarar 2009.

Bayan koyarwar addinin da ya dauki tsawon lokaci yana yi, malamin ya yi tashe wajen taimaka wa al’umma ta bangaren neman lafiya daga shafar aljanu.