Iyalan sananen malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Usma Bauchi sun karyata jitajitar da ake yadawa cewa ba shi da lafiya yana kwance, inda suka ce shehin yana nan lafiya kalau.
Daya daga cikin Hadimansa Alhaji Sanusi Ahmad Dahiru ya ce shehin yanan lafiya, kuma yanzu haka ma ya tafi aikin umarah ranar Juma’ar da ta gabata kuma yana cikin koshin lafiya.
Sanusi ya ce a a kwanakin baya ma wadansu mutane sun ta yada jita-jitan cewa ya rasu.
Sai ya roki Allah Ya ja kwanan shehi Ya kara masa lafiya.
Wannan karin hasken yana zuwa ne bayan wasu kafafen watsa labarai sun ta yada jita-jitar cewa shehin yana kwance ba shi da lafiya.