Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta bayyana cewa za ta karɓi sabbin jiragen sama guda 49 kafin ƙarshen shekarar 2026.
Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron Injiniyoyin Jiragen Sama na shekarar 2025 da aka gudanar a hedikwatar NAF da ke Abuja.
- Matan da aka kubutar a Neja sun dawo da juna-biyu da jariran ’yan ta’addan da suka sace su
- Yadda za a ci gaba da zaman karɓar gaisuwar Buhari
Ya ce jiragen da ake sa ran karɓa na zamani ne, kuma suna buƙatar kulawa ta musamman da horarrun ma’aikata kafin su yi aiki yadda ya kamata.
Air Marshal Abubakar, ya ƙara da cewa yanzu haka kusan kashi 72 cikin 100 na jiragen saman rundunar suna aiki.
Amma manufarsu ita ce wannan adadi ya kai zuwa kashi 90 cikin 100 kafin ƙarshen zango na hudu na shekarar 2025.
Ya bayyana cewa wannan ci gaban ya samu ne saboda sanya kuɗi da ake yi wajen siyan kayan gyara, kayan aikin gyaran jirgi, da kuma horar da ma’aikata.
Taken taron shi ne: “Inganta Gyaran Jiragen Sama a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta Hanyar Kyakkyawan Tsarin Kula da Jirage da Haɗin Gwiwa da Abokan Hulɗa.”
Taron ya mayar da hankali ne wajen gano hanyoyin da za su inganta gyaran jirage da kuma tabbatar da cewa dukkaninsu suna cikin lafiya don yin aiki a kowane lokaci.