Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.
Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 98 a duniya — ranar 2 ga watan Almuharram 1444 Hijiriyya — yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani.
- Buhari ya nada wan matarsa shugabancin kamfanin buga kudi na Najeriya
- Sannu a hankali Najeriya na komawa mulkin kama-karya – Jonathan
A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.
Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’anin
Yana daga cikin Halifofin Sheikh Inyass
Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.
Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.
A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.
“To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.
“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.
“Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.
“An haife ni ne a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira, a ranar Laraba.”
‘Yadda na mayar da karatun Alkur’ani sana’ata’
Ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.
“A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karatun Alkur’ani da karanta Salatul Fatihi da tasbihi da istigfari da salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori,” in ji shi.
Kwarewar Sheikh Dahiru Bauchi
Da aka tambaye shi kan fannonin ilimin da ya fi kwarewa, shehin malamin ya ce, “Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Alkur’ani kuma ta hannunsa ne na karbi Darikar Tijjaniya.
“Shi mahaifina ya karbi Darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba, daga baya sai mahaifina ya ba ni izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Alkur’ani mai girma.
“Bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkur’ani, daga nan kuma sai bangaren Tafsiri, a nan malaman Tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su.
“Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiran sa Tlimin Tarbiyya.
“A nan ma masu irin ilimin kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare.
“Sauran ilimomi kuma ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu, duk ina tattabawa,” inji shi.
‘Dalilin da nake buga misali kan duk tambayar da aka yi min’
Da aka tambayarsa cewa jama’a na mamakin yadda idan aka yi masa tambaya sai ya ba da misali kafin ya bayar da gundarin amsar, sai ya ce, “Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane.
“Idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su.
“Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa.”
Shehin malamin ya zama masanin Tafsirin Alkur’ani Mai Girma wanda ya samu lambobin yabo a wannan bangaren.
Ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori daban-daban a Najeriya da ma kasashen waje.
Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi lambar yabo ta Digirin girmamawa, sannan Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR.
Nasarorin Sheikh Dahiru Bauchi
Ga wasu daga cikin nasarorin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekarunsa:
- Ya musuluntar da dubban mutane
- A duk lokaci bayan lokaci yakan karanta Alkur’ani kuma yana yin saukar Alkur’ani a kwana biyu
- Ya ba da lazumin Darikar Tijjaniyya wa dubban mutane da dama a fadin duniya
- Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1500 a Najeriya da sassan Afirka
- Sama da mutum 140,924 sun haddace Alkur’ani a makarantunsa a fadin Najeriya
- Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya
- Mutum ne mai kishin kasarsa Najeriya wanda aduk lokacin da ya bude baki zai yi addu’a sai ya roki Allah Ya ba kasar zaman lafiya da kwanciyar hankali
Bugu da kari, malamin yana cikin wadanda suka fi kowa dadewa suna tafisirin Alkur’ani da watan azumin Ramadan.
Masallacin da yake tafsirin da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna, na daya daga cikin manyan masallatan da ke cikin garin, kuma za a iya cewa a tsawon shekaru, malamin yakan zauna a garin kusan fiye da a ko ina.
Wani bincike da wani wanda yayi Nazari kan rayuwar malamin ya kuma rubuta littafi a kansa mai suna Shehu Dahiru Bauchi Ginin Allah, shekaru uku da suka wuce, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, ya ce
Daya daga cikin almajiran shehin, Mallam Ahmad Tijjani Kolo, ya ce a yanzu an sami karin mahaddata a cikin zuri’arsa, inda yanzu suka doshi 300. Ya ce da wahala a sami mai irin wannan a tarihi.
Shugaban Kungiyar Daliban Sheikh Dahiru Bauchi, Mallam Ibrahim Imam Ismaila, ya ce a tarihi babu wanda ya taba samun irin baiwarsa.
‘Rayuwarsa gaba daya makaranta ce’
Shi kuwa Daraktan Wakafi a Hukumar Shari’a na Jihar Bauchi, Mallam Ahmad Tijjani Sa’id, ya ce rayuwar shehun malamin gaba dayanta makaranta ce.
Ya kuma ce malamin ya yi tafiya daga Arewa har kasashen Kudu a kan jaki da doki don yada addinin.
Sannan ya yi tafiya a kan keke zuwa kauyuka da dama kamar Tafawa Balewa da yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma don yada addinin Musulunci.
‘Gidajensa 1,000 da ake zama kyauta’
Malam Ahmad Tijjani Sa’id ya ci gaba da cewa babu abin mamaki cikin sha’anin malamin kamar yadda yake daukar nauyi ba tare da jin tsoron hidima ba.
“Yana da gidaje fiye da dubu daya a fadin kasar nan, amma ba inda ake haya, bayin Allah masu neman ilimi yake zubawa a ciki kyauta.
“Jama’ar da yake ciyarwa Allah kadai Ya san adadinsu. A kullum idan Shehi zai fito zai sallami baki fiye da 3,000 da suka zo ziyarar sa daga ciki da wajen Najeriya, kuma za ka samu dalibansa ya yi musu auren fari ya musu suna kuma bai gaji ba.
“Ya maka mace ta biyu ya dauki nauyinku. Ire-iren wadannan halaye na Shehi da wuya ka samu wanda zai iya yin haka.”