✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sheikh Ahmed Lemu ya riga mu gidan gaskiya

Mashahurin malamin Musuluncin ya rasu yana da shekara 91

Shahararren malamin Mususlunci Sheikh Ahmed Lemu ya riga mu gidan gaskiya a safiyar ranar Alhamis.

Iyalan mashahurin malamin kuma alkali ne suka sanar da haka ta bakin dansa, Nuruddeen Lemu, wanda ya ce Sheikh Lemu ya rasu ne a Minna, Jihar Neja.

“Inna lillahi wa inna liayhi raji’un; Allah Ya yi wa mahaifinmu, Mai Shari’a Dokta Sheikh Ahmed Lemu rasuwa da sanyin safiyar yau (Alhamis) a Minna; Nan gaba za a sanar da shirye-shiryen jana’iza,” inji sanawar da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, hakika babbar alfarma ce a gare ni da na kasance diyar wadannan mutane,” kamar yadda diyar mamacin, Maryam Lemu ta wallafa inda ta sanya hoton mahaifin nata da mahaifiyarsu.

Tuni jama’a suka shiga mika ta’aziyya tare da alhinin rasuwar Sheikh Lemu, wanda suke ta yi wa addu’o’in samun rahamar Allah.

“Inna lilahi wa inna liayhi raji’un. Allah Madaukakin Sarki Ya sada da ta Fiyayyen Halitta. Amin,” inji Ministan Harkokin Gida na Najeriya, Rauf Aregbesola.

Muhimman abubuwa game da Sheikh Ahmed Lemu

 1. Shi ne alkali na farko a Kotun Daukaka Kara ta Shar’ia Musulunci a Jihohin Sakkwato da Neja a shekarar 1976-1977.
 2. Ya zama Babban Alkalin Kotun Daukaka Karar Shari’a a Jihar Neja a 1976-1991.
 3. Ya  bayar da gagarumar gudunmuwa a tattaunawar samar da tsaro da zaman lafiya bayan samun matsalolin tsaro a Arewacin Najeriya.
 4. Ya shekara sama da 50 yana koyarwa tare da yada addinin Islama.
 5. Malami ne na harshen Larabci, Turancin Ingilishi da kuma Ilimin Musulunci.
 6. Ya koyar a makarantar GSS Bida, Jihar Neja da kuma makarantar harshen Larabci ta SAS da ke Kano.
 7. Ya rika mukamai daban-daban daga malamin aji har ya kai ga matsayin Darakta daga 1953 zuwa 1976.
 8. Ya zama kwararren mai bayar da shawara kan ilimi na Jami’ar Osogbo a 2009.
 9. Mutum ne mai takawa da kira ga rungumar juma.
 10. Mamba ne a hukumomin Musulunci a fadin duniya.
 11. Ya gabatar da laccoci da darussa da tarukan kara wa juna sani a kokarinsa na yada ilimi, ci gaba da kuma Musulunci
 12. Ya wallafa litattafai aka shafe shekaru ana amfani da su domin fahimtar addinin Islama a Najeriya.
 13. Ya kafa kungiyoyi, makarantu da gidauniyar Musulunci da ta kai ga hadin gwiwa da Bankin Musulunci wurin bunkasa ilimi a Najeriya.
 14. Babban jagora ne wurin kare hakkokin mata Musulmi.
 15. Kokarinsa ya kai ga kafa kungiyoyin mata Musulmi a Najeriya, yada zaman lafiya da kuma yaki da rikice-rikice tsakanin dariku.
 16. Shi ne ya kafa cibiyar yada Musulunci ta Islamic Da’awa Institute domin yaki da tattsauran ra’ayin addini.
 17. An ba shi kyatuttuka da dama daga hukumomi da cibiyoyi na cikin gida da ma na duniya saboda hidimarsa ga addinin Islama.
 18. Yana da Digirin Digirgir na Karramawa guda uku: Jami’ar Usmanu Danfodiyo (1996); Jami’ar Osogbo (2011) da jami’ar Al-Hilal (2013).
 19. Shugabannin Kasar Najeriya sun ba shi lambar girmamawa ta kasa: Abdulsalami Abubakar (1999); Olusegun Obasanjo (2001).
 20. A 2014 ya samu Kyautar Sarki Faisal na Kasar Saudiyya kan yi wa Addinin Musulunci Hidima.
 21. A shekarar ce kuma aka nada shi Shugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar Bayar da Tallafin Musulunci ta Duniya.

Tarihin iliminsa

 1. An haife shi a ranar 12 ga watan Disamba, 1929, shekara 91 da suka gabata.
 2. Bayan fara karatun allo a 1932, an sa shi a makarantar elemantare wadda ya kammal a 1939.
 3. A 1948 ya kammala kwaleji a mahaifarsa, Lemu, Jihar Neja ta yanzu.
 4. A Lemu ya yi Makarantar Shari’a (School of Arabic Studies a yanzu) inda ya samu karamar shaida a 1950.
 5. Sannan a 1952 ya samu shaidar koyarwar ta Grade Two a harshen Larabci, Ilimin Musulunci da Shari’a da Tarbiyya.
 6. 1954 ya je Jami’ar London a kasar Birtaniya inda ya karanci Tarihi da harsunan Larabci, Hausa da Fasha a 1961.
 7. A 1964 ya samu Digiri a kan hallayar ’yan Afirka daga Jami’ar.
 8. Sheikh Ahmed Lemu miji ne ga mashahuriyar mai da’awar kuma marubuciyar Musulunci, Aisha Lemu.