✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Abduljabbar ya nemi afuwa

Ina neman afuwa ba a fahimce ni ba ne.

Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara, ya nemi afuwar Musulmin da suka fahimci cewa shi ne ya kirkiri kalaman batanci ga Fiyeyyen Halitta da ake zargin sa da yi, yana mai cewa ba a fahimce shi ba ne.

Neman afuwar na zuwa ne bayan kwana guda da fafata wata mukabala tsakanin shehin malamin da wasu malamai a Jihar Kano.

Cikon wani sakon murya da ya fitar a ranar Lahadi, Abduljabbar ya ce, “Idan har wadannan kalamai daga ni suke, kirkirar su nayi, babu su a nassi, to lallai haka kadai ya isa babban laifi a gare ni na gaggauta tuba.

“Idan kuma ba daga ni suke ba, a haka na ciro su daga cikin litattafan Hadisi, to wannan kuma wani babban kalubale ne ga dukkan Musulmi su farka domin fitar da wadancan Hadisan karya don tabbatar da tsarkin da Annabin mu yake da shi.

“Ya zama wajibi mu mike tsaye domin ganin cewa ba a rusa mana addininmu ba.

“Har wa yau, idan sun kasance daga gare ni, to abu na farko shi ne ina neman gafarar Allah, sannan ina neman afuwa daga jama’ar Musulmi kuma na janye kalamaina.

“A yayin da wasu ke zargin cewa ni na kirkiro Hadisan da kaina, to kuwa mutane da dama sun bata domin kuwa a haka na ciro su daga cikin nassoshin da aka gurbata.

“Amma wadanda ke sauraron karatuttukana kai tsaye sun fahimci yadda abin yake.

“Saboda haka wannan ba abu ba ne da mutum zai iya fayyacewa a cikin mintuna kadan, kuma shi ne dalilin da na ce babu adalci a muhawarar da aka yi a ranar Asabar.

“Saboda ba a bani wadataccen lokacin da zan fito da abin fili ba yadda kowa zai fahimta.

“Ba zan iya fito da su ba a cikin mintuna goman da aka ba ni, ba wai don babu su ba ne,” a cewar malamin.

Kalaman nasa na nuni da cewa har yanzu malamin yana nan a kan bakarsa game da ikirarin da yake yi cewa ya ciro kalaman ne daga littafan Hadisi.

A Asabar da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Kano ta shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da wasu malamai daga bangarorin akida daban-daban inda suka tafka muhawar kan kalaman nasa.

Sai dai Sheikh Abduljabbar bai gamsu da zaman ba saboda, a cewarsa, ba a ba shi isasshen lokacin da zai kare kansa ba.

Alkalin da ya jagoranci muhawarar, Farfesa Salisu Shehu, ya ce malam Abduljabbar ya gaza amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa.

Farfesa Salisu wanda shi ne shugaban Cibiyar Addinin Islama da Tattaunawa Tsakanin Addininai ta Jami’ar Bayero, ya ce “bisa mukabalar da aka yi, Abduljabbar ya cakuda bayanansa, kuma wasunsu ba a kan doron Ilimin Hadisi yake gina su ba.

“Na yanke hukunci Malam Abduljabbar bai bayar da amsoshin tambayoyin da wadannan malamai suka yi masa ba,” inji shi.

Tuni dai Gwamnatin Kano ta fara shirin gurfanar da malamin a gaban kuliya, kan zargin kalaman batanci da kuma na tunzura al’umma.

Haka kuma, Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kano, ta aike wa malamin wasikar neman ya bayyana a babban ofishinta da ke Bompai a ranar Litinin.