Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya yi afuwa ga fursunoni 23 albarkacin cikar jihar shekaru 28 da samuwa.
Bugu da ƙari, ya rage wa wasu fursunoni biyu hukuncin daurin rai-da-rai zuwa shekaru 15, sannan ya sauya wa wasu biyu hukuncin kisa zuwa na daurin rai-da-rai.
Shagulgulan tunawa da cika shekaru 28 da samun Jihar Gombe ya zo ne a daidai lokacin da ke bikin cika shekaru 64 da samun ’yancin kai.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi afuwa ga fursunonin ne a gidajen yari a fadin jihar la’akari da shawarwarin da Kwamitin Shawara kan ’Yanci da Afuwa da ya jiha.
- Ranar ’Yanci: Jihar Borno ta takaita bikin zuwa addu’o’i
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Shaukin Ranar Samun ’Yancin Kai?
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Fadar Gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, ya ce “an kuma rage wa wani fursuna hukunci zuwa shekaru 10, sannan an rage wa wasu fursunoni hudu da ke jiran kisa hukuncin zuwa ɗaurin shekaru 15.
“Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana fatan cewa afuwar za ta bai wa waɗannan mutane dama ta gyaran hali da zama na gari a cikin al’umma, wanda hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe.”