✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shehu Kangiwa: Tuna gwarzo bayan shekara 37

Marigayi Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Shehu Muhammad Kangiwa, shi ne Gwamnan farar hula na farko a tsohuwar Jihar Sakkwato ya rasu ne a wani munmunan…

Marigayi Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Shehu Muhammad Kangiwa, shi ne Gwamnan farar hula na farko a tsohuwar Jihar Sakkwato ya rasu ne a wani munmunan hadari mai sosa rai shekara 37 da suka wuce. Ya rasu sanadiyyar raunin da ya samu  bayan ya fado daga saman doki lokacin da suka buga gasar kwallon Polo a garin Kaduna. Hakika ba a yi wasu bayanai ko rubuce-rubuce na a-zo-a-gani game da shi kansa ko ayyukansa ba bayan rasuwarsa. Bai kamata a manta da wannan jarumi ba, musaman idan har abin da ake fada a cikin taken kasa abin dogaro ne “The Labour of our heros past shall neber be in bain” wato “ Fadi tashin magabatanmu ba zai taba zama banza ba.”

Marigayi Shehu Kangiwa wanda ya rasu 17 ga watan Nuwamba 1981 ya yi aiki a matsayinsa na Gwamna ne na   tsawon shekara biyu da wata daya da kwana 16,  amma cikin  wannan kankanen lokaci babu fannin  da gwannatinsa ba ta taba ba wajen aiwatar da ayyukan ci gaban jiharsa.

Ranar 28 ga watan Maris 1980, lokacin da ya gabatar da kasafin kudinsa ga Majalisar Jihar Sakkwato, kasafin da ya yi wa taken “Kasafi na gaskiya domin mutanen karkara.” Wannan kasafi ya sa an kirkiro sabuwar Ma’aikatar Raya Karkara kuma domin tabbatar da nasarar wannan ma’aikata, sai Gwamna Kangiwa ya bar ta a karkashin kulawarsa domin  ya ga cewa an samu raguwar kwararar mutanen karkara daga kauyuka zuwa birane.

Manufar Shehu Kangiwa ita ce ya ga cewa an tallafa musu  wajen habaka ayyukansu na noma da samar musu da abubuwan more rayuwa da bunkasa harkokin tattalin arziki da walwalarsu domin inganta rayuwarsu

A lokacin rayuwarsa, mutane suna yi wa Shehu Kangiwa kallon mutum mai basira da hangen nesa da kyauta da yin haba-haba da jama’arsa. Kwarjininsa ya kara fice tare da karuwa a wajen jiharsa lokaci taron gwannonin Jam’iyyar NPN.

A fagen siyasa kuma takwarorinsa na kallonsa a matsayin mai dimbin hikimomi da dabarun shawo kan magoya baya musaman a yayin kamfe. Mutum ne mai sha’awar wasannin motsa jiki kamar kwallon dawaki wato Polo wanda shi ne sanadiyyar kafuwarta a Sakkwato.

Da yawa daga cikin  abokansa na kallonsa a matsayin mutum mai kwazo da  cika alkawari. Shahararen Mawakin Hausa marigayi Alhaji Sani Aliyu Dandawo, yakan kira shi da “Shehu mai fada da cikawa ne,” akidar da aka rasa a wajen ’yan siyasar wannan lokaci da muke ciki.

Lokacin da aka kawo gawar  marigayi Shehu Kangiwa zuwa Sakkwato daga Kaduna, fiye da jiragen sama 25 ne suka sauka a filin jiragen sama na Sakkwato dauke da dubban mutane masoyansa da abokansa da ’yan siyasa daga ciki da wajen Najeriya domin su halarci jana’izarsa. Wannan ya nuna irin kyakkyawan zaman da Shehu Kangiwa ya yi da jama’a a ciki da wajen Najeriya.

Alhaji Isa Kangiwa (Mutawallen Argungu) shi ma Allah Ya yi masa rasuwa bana) wanda shi ne Kwamishinan Gidaje da Muhalli lokacin gwannatin Shehu Kangiwa kuma ajinsu daya tun suna yara, ya bayyana marigayi Kangiwa da cewa “Mutum ne wanda ya fi kowa basira a cikin ajinsu tun suna yara.”

Lokacin rayuwarsa, marigayi Shehu Kangiwa ya samu nasarori da dama.

A fagen ilmi, Jihar Sakkwato wadda ta hada da Jihar Kebbi da  Zamfara a yau duk sun shaidi bude makarantu da daga darajojin wasu zuwa manyan makarantu. Sannan yawan dalibai masu shiga makaranta sun karu, baya ga samuwar ingantuwar yanayin koyarwa da karatu ga malamai da kuma dalibai.

Lokacin gwannatin Shehu Kangiwa ta fito da shirin gine-ginen gidajen ma’aikata da otel-otel da ofisoshi inda aka gina Sakatariyar Giginya (Shehu Kangiwa Sakatariya) da gidajen kwamishinoni na Titin Sama da gidajen ma’aikata na Unguwar Bado. Sai otel din Giginya da Shukura. Lokacinsa ne aka gina gidan tarihi mai suna Wazirin Junaidu History Bureau da kuma dakin karatu na jihar wato State Library wanda ke titin Sultan Abubakar  Sakkwato da sauransu.

Gwannatin Kangiwa ta samar da hanyoyin mota manya da kanana da suka hada babban birnin jihar da sauran garuruwa da kauyuka.

Marigayi Shehu Kangiwa ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya tara.

Da yake bayani kan yadda rayuwarsu ta kasance bayan rasuwar mahaifinsu, daya daga cikin ’ya’yansa Malam Ibrahim ya koka cewa rayuwar dai ta kasance ba dadi sai hamdala ga Allah. Ya ce dukan aminan Babansu sun kaurace musu sai kalilan daga cikinsu. Ya ce daga cikin abokan Babansu masu ziyartar gidan har yanzu akwai Kanar Dangiwa Umar (mai ritaya) da Sanata Garba Illah Gada da Injiniya Murtala Zauro da kuma marigayi Alhaji Umaru Ali Shinkafi (Marafan Sakkwato).

 

Ana iya samun Ahmad N. Argungu ta email: [email protected]