A baya mutum zai dauka rikice-rikicen da ke yawan faruwa a Jihar Filato suna da nasaba da kabilanci da addini tsantsa, sai dai bayan sake duba na musamman, an fahimci ba a nan kawai lamarin ya tsaya ba.
A yanzu dai bincike ya gano cewa harkar shaye-shayen muggan kwayoyi a tsakanin matasa da ke ta yaduwa kamar wutar daji na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa rikice-rikicen.
- Abin da ya sa na fice daga PDP —Abba Gida-gida
- Saudiya da Qatar sun koka kan rashin kulawa da rikicin Gabas ta Tsakiya
Gano wata gawa da aka yi a shekarar 2019 a yankin Unguwar Damisa da ke Dutse-Uku a yankin Karamar Hukumar Jos ta Arewa ya haifar da rikice-rikice, ta yadda yawancin Kiristocin da suka tafi wuraren bautarsu ba su iya dawowa gida ba a lokacin.
Rikici ya balle ba a unguwar da aka gano gawar ba kadai, hatta sauran yankunan da ke kewayen wurin sai da rikicin ya shafa.
Wuraren da suka hada da Dutse-Uku da Cele-Bridge da Tina Junction da kuma Rikkos, duka rikicin ya shafe su inda bayan kashe wasu da kona gidaje da aka yi, an kuma jikkata wasu da dama tare haddasa wasu suka zama ’yan gudun hijira bayan raba su da muhallinsu.
Duk da cewa yankin ya yi kaurin suna musamman kasancewarsa mahada ce da ta raba mazaunan ta hanyar addini da kabila amma kuma an gano rikicin na da alaka da kasancewar wurin wata matattarar masu shaye-shayen kwayoyi da bushebushen tabar wiwi.
Rikicin ya samo asali ne bayan barkewar takaddama tsakanin mashayan inda daya ya rafke abokin husumarsa abin da ya janyo rasa ransa bayan wani lokaci.
Bayan gano gawar ce daga baya sai lamarin ya rikide zuwa rikicin addini, inda matasa suka fara daddasa shingaye suna tare mutane tare da rafke duk wanda ya saba da addininsu.
Akwai ire-iren wadannan takaddamar da suka rikide zuwa rikicin addini da na kabila ta yadda matasan da ba su da wata masaniya kan abin da ya faru nan da nan za su mayar da shi rikicin da in ba a dauki matakin gaggawa ba sai ya yadu zuwa wasu sassan, wanda hakan na daga cikin abin da shaye-shaye ke haifarwa.
Idan har aka dakile shayeshayen kwayoyin da aka haramta tu’ammuli da su a tsakanin matasa, wanda aka yi amanna su ke haddasa su yin wasu abubuwan da ba su dace ba, babu makawa za a shawo kan kaso mai yawa na irin wadannan matsalolin.
Damuwa da irin haka ne ya sa a bara wata cibiya mai kokarin tallafa wa musamman matasa mai suna Cibiyar Tallafi ta Zishiya ta tashi tsaye wajen kokarin hana matasa harkar kwayoyi a fadin Jihar Filato gaba daya ba wai garin Jos ba kawai don dakile harkar shaye-shaye.
‘A sanya illar ta’ammali da muggan kwayoyi a manhajar koyarwa’
Babban Daraktan Cibiyar, Biolet Kaburuk, ta yi kira a wajen taron bita na kwana hudu da aka shirya wa kananan hukumomi 17, cewa gwamnati ta yi kokari ta sanya batun ta’ammali da muggan kwayoyi a cikin tsari da manhajar koyarwa don taimakawa wajen dakile illar kwayoyin a cikin jama’a.
Kaburuk ta kuma bayar da shawarar bincika dalibai a kai a kai tun daga makarantun firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare da ke jihar, inda ta ce akwai bukata matuka na ilimantar da yara hadarin amfani da muggan kwayoyi ko harkokin maye don su guje su.
Da yake tofa bakinsa kan hatsarin da shaye-shaye ke dauke da shi, wani mazaunin Unguwar Rogo da ke Jos, Haruna Yusuf Abba ya shaida wa wakilinmu cewa mafi yawan abin da ke haddasa rikici da tashin hankali ko duk wani nau’i na laifi yana da alaka da harkar shaye-shaye, don haka ya ce dole ne a tashi tsaye don wayar wa matasa kai da kuma ilmantar da su illa da hatsarin ta’ammuli da kayan maye.
Abba, wanda mawallafi ne kuma mai rajin kira ga matasa kan shiga a dama da su kan harkokin shugabanci, ya ce matasa a garin Jos na tu’ammuli da kayan maye dangin tabar wiwwi da kwayar tiramol da kodin, da banalin da rafinol da sauran nau’o’in shayeshaye da bushe-bushe.
“Mafita kawai ita ce, gwamnati ta rika bibiyar lamarin tare da hukunta masu sayar da kwayoyin a shagunan sayar da magunguna a cikin al’umma.
Kuma yana da kyau a san cewa hatta wasu jami’an tsaron da aikinsu ne dakile harkar shaye-shayen amma kuma da hannunsu dumu-dumu cikin lamarin, wanda hakan ne ya sa ba su iya hukunta matasan da ke shaye-shayen ko masu sayar da ita hukuncin da ya kamata,” inji shi.
Shi ma Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), bangaren matasa reshen Jihar Filato, Markus Kanda, ya bayyana yadda harkar kwaya ke rikita tunanin matasa tare da juyar da hankalinsu har su aikata abin da bai dace ba.
Ya ce masu shaye-shayen na cikin barazanar kamuwa da cututtukan kwakwalwa da suka hada da tabin hankali.
“Yayin da matasa suka sha wani abu kwakwalwarsu da tunaninsu kan juya su zamo suna tunani daban da na masu hankali, ta yadda suke zama wadanda cikin sauki ake amfani da su wajen ayyukan tashin hankali,” inji shi.
A watan Disamban bara ma wasu masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin kabilu da na addini sun bayyana harkar shayeshaye a matsayin lamarin da ke haifar da rikici a garin Jos, a wajen wani taron da suka gudanar.
A cikin takardar bayan taron da suka fitar, sun yi kira ga jami’an tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su dakatar da harkar shaye-shaye a tsakanin matasa, kasancewarsa abin da ke haifar da tashin hankali a cikin al’umma.
“Mafita kawai ita ce, gwamnati ta sake duba lamarin tare da tabbatar da ana hukunta masu sayarwa da irin wadannan kwayoyin,” inji sanarwar.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel Ogaba ya tabbatar da cewa shaye-shayen a matsayin abubuwan da ke taimakawa wajen haifar da rikice-rikice a Jihar ta Filato.
Ya ce ’yan sanda na aiki kafada da kafada da Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) don magance lamarin.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun rubuta dukkanin matattarar shan kwayoyin kuma suna musu dirar mikiya a kai-a kai.
Hakazalika shi ma Kakakin Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya na ‘Operation Safe Haben (OPSH)’ da ke Jos, Manjo Ishaku Takwa, ya bayyana matasan da ke haifar da rikici a matsayin masu harkar shaye-shaye kamar yadda rundunar ta gano irin kwayoyin a wajen matasan da ta kama.
Ya ce da yawan matasan suna shan kwayoyin ne a maboyarsu, ba suna amfani da kwayoyin ne a lokacin zartar da muggan ayyukan na su ba da suke kaddamarwa a kan mutane da dukiyoyinsu.
Ya ce a duk lokacin da suka kama matasa suna damka wa ’yan sanda ne domin ci gaba da bincike tare da daukar mataki a kansu.
Shi ma Chrisantus Madaki na Rundunar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Filato, ya dangana samuwar rikici a Jihar Filato da shan muggan kwayoyi.
Ya ce wannan ne dalilin da ya sa mutanensu ke kai samame maboyar masu shaye-shayen. A kokarin magance matsalar a jihar ce kungiyar PARE ta makiyaya ta wayar da kan matasa a kananan hukumomin Riyom da Bokkos kan matsalar.
Ita ma Shugabar NDLEA ta Karamar Hukumar Mangu da ke jihar ta Filato, Ku’ulyidam Hassan, ta ce za a iya shawo kan matsalar tashin hankali idan har aka shawo kan shaye-shaye a tsakanin matasa.
Ta yi kira ga al’ummomi da su rika kawo rahoton duk abin da ya shafi harkar shaye-shaye ga hukumarsu domin daukar matakin gaggawa a kai.