✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shayarwa ga mace ma’aikaciya

Amsa: Hakika wannan tambaya ta na da muhimmanci ga lafiyar jarirai wadanda iyayensu ke aiki, ganin wannan makon ne hukumomin lafiya a ko’ina a duniya…

Amsa: Hakika wannan tambaya ta na da muhimmanci ga lafiyar jarirai wadanda iyayensu ke aiki, ganin wannan makon ne hukumomin lafiya a ko’ina a duniya suka ware domin fadakarwa akan muhimmancin shayarwa. Abin takaici shi ne duk da ci gaba da aka samu a duniya ta bangaren aikin mata ta hanyar ba su hutun haihuwa da na shayarwa, da ware wurare na musamman domin kula da jariransu, a wannan kasa har yanzu ba a baiwa mata ma’aikata irin wadannan hakkoki da saura musamman a kananan ma’aikatu.

To idan ana wannan muhawara wasu sa ce e uwa ma’aikaciya za ta iya barin jaririnta a gida masu rainon su rika dama mu su madara ko ta shanu ko ta waken soya ko ta formula. Wannan shawara ce amma gurguwa. Wasu kuma sukan dauki tsattsauran ra’ayin hana matar aiki ma gaba daya saboda lura da shayar da jariri. To amma dai a wannan zamani da ya kamata mace ma ta samu nata abin hannu ko don taimakawa a gida, wannan ma gurguwar shawara ce.

Mafita da masana lafiyar jarirai suka fitar ita ce ta ci-gaba da shayarwar kuma a je aiki. To a irin wuraren da ba sa barin a je musu da jarirai ya uwa za ta yi? Mafita wadda ba ita dai aka so ba ita ce ta matse ruwan nono a kwalbar feeder a bari a gida don ba wa jariri duk lokacin da ya bukata. Wannan wasu za su ji kamar da sauki abin, domin fa akwai ‘yar wahala. To amma dai ita ce mafita mafificiya. Abinda ya sa aka ce akwai ‘yar wahala shi ne da dama mata iyaye sai an koya musu yadda ake matso ruwan mama a asibiti, wasu ma saboda zafi da gajiyarwa da sun fara za su bari. To domin haka ne akan ba su shawara idan ba za su iya matsa da hannu ba to dole sai sun sayi wani dan famfon tatsa mai kama da feeder jaririn, wanda akan samu a manyan kyamis-kyamis.

Bayan an tatso ruwan nonon a wannan famfo sai a juye shi a cikin feeder jaririn. Idan ‘yan awoyi ne da ba su wuce uku zuwa biyar ba, kuma gari ba zafi, a kwano cooler kawai za a sa feeder har sai jariri ya bukata, idan ma ya rage, a mayar cooler. Idan kuma tsawon yini ne aikin to kusan dole sai an cika feeder biyu ko uku, kuma ba a cooler za a sa su ba, sai dai na’urar fridge. Sa’annan kullum idan aka wanke feeder jaririn sai an tsoma su a tafasasshen ruwa domin tsabtace su da kiyaye jariri daga kwayoyin cuta saboda damuke-damuke da masu shayarwa suka yi. To kin ji wahalhalun wannan mafita, amma idan aka daure za a iya.