A makon farko na watan Agustan da ya gabata ne aka gudanar da bikin makon shayar da jarirai nonon uwa na duniya karo na ashirin. Bikin dama ce da kwararru a harkar lafiyar kananan yara na kowace kasa ke amfani da ita domin nanata muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa tare da warware wasu mas’aloli da suka danganci hakan. Taken bikin na bana shi ne: “Waiwayen baya, don fuskantar gaba.”
A Najeriya, shayar da jariri nonon uwa ya kasance abu mai asali, wanda kusan za a iya cewa babu wata kabila da ba ta shayar da jariranta nonon uwa. Wani bincike na Hukumar NDHS (2008), wanda aka gudanar a karkashin Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ya nuna cewa, mafi yawan kananan yara a Najeriya na samun shayar da nonon uwa har na tsawon wata goma sha takwas kafin a yaye su.
Sai dai alkaluman binciken sun nuna cewa, kashi goma sha uku ne cikin dari kacal na jariran ke samun shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida, kamar yadda hukumomin lafiya suka bukaci a yi.
Don haka a inda gizo yake sakar shi ne, lokacin da ake fara shayarwar, da yanayin yadda ake gudanar da ita.
Wani rahoto da wata kungiyar jinkan kananan yara ta Sabe the Children ta wallafa a bana, ya nuna cewa, kimanin kananan yara miliyan goma sha daya ne a Najeriya ke fama da matsalolin lafiya masu dangantaka da karancin samun ingantaccen abinci, kuma akwai yiwuwar alkaluman za su iya wuce miliyan goma sha uku nan da shekara ta 2020, in har ba a dauki matakan da suka kamata ba. Rahoton ya tabbatar da cewa shayar da nonon uwa na da matukar rawar takawa wajen rage wannan matsala.
ka’idojin sharya da nonon uwa kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya suka tabbatar sun hada da dora jarirai a kan nonon uwa, tun daga sa’a ta farko bayan haihuwa ba tare da an zubar da ‘Dakashi’ ba. Dakashi shi ne nonon farko mai kauri, wanda yake fara zuwa bayan an haihu. Za a ci gaba da bai wa jarirai nonon uwa zalla ba tare da an hada da ba su ruwa ba, har sai sun kai wata shida da haihuwa, sannan a fara hada musu da ingantattun abinci masu ruwa-ruwa har sai su kai akalla shekara biyu da haihuwa, sannan a yaye su.
Dalilai da dama ne suke sa iyaye mata suke kasa aiwatar da wannan tsari na shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida. Daga ciki akwai rashin sanin muhimmancin hakan ga kiwon lafiya da kafewa a kan fahimta marar tushe da kuma rashin isassun dokoki na kasa, wadanda za su karfafa gwiwar iyaye mata don aiwatar da tsarin.
Shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida na da matukar muhimmanci ga lafiyar jariri, kasancewar nonon uwa tatacce kuma tsabtataccen abinci da Allah (SWT) Ya tanada don jarirai, ya kunshi duk sinadaran abinci wadanda jarirai ke bukata wajen gina jiki da samar da kuzari da kuma ba da kariya daga kwayoyin cuta.
Bincike ya tabbatar da cewa shayar da nonon uwa na iya rage kamuwa da ciwon yunwa, wato Tamowa da sauran cututtuka masu alaka da karanci ko ingantaccen abinci.
Kuma ya kamata mu sani cewa, duk wani nau’in abinci da ake amfani da shi a madadin nonon uwa ba zai taba samun inganci, kamar na nonon uwa ba, duk adadin kudin da za a kashe wajen hada shi. Ko ba komai, akwai hadarin shigar kwayoyin cuta yayin hada abincin ko wajen ajiya da kuma wajen bayarwa.
Shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida na taimaka wa uwa wajen komawar mahaifa da wuri bayan haihuwa, wanda hakan zai taimaka jikinta ya murmure tare da rage yiwuwar sake daukar wani cikin da wuri.
Shayar da nonon uwa na kara shakuwa da kauna tsakanin uwa da jaririnta. Kasancewar nonon uwa abu ne daga Allah, wanda ba sayensa ake yi ba, shi kansa mai gida zai samu saukin dawainiya, ta yadda zai iya amfani da rarar kudinsa don yin wata hidima ta iyali, maimakon sayo madara da za a hada wa jariri.
Tunanin da wadansu ke yi na cewa wai idan ba a bai wa jariri ruwa zai galabaita, sam ba gaskiya ba ne. Domin binciken masana ya tabbatar da cewa kashi 88 cikin 100 na sinadaran da nonon uwa ya kunsa ruwa ne. Don haka jarirai ba sa bukatar karin wani ruwa, bayan wanda yake samu daga cikin nono. Iyaye da dama wadanda suka gwada shayar da nonon uwa zalla na wata shida, sun tabbatar da ingancin hakan wajen kara lafiyar jarirai da kuma tasirin da hakan wajen girman jikinsu da kuma kaifin kwakwalwarsu bayan sun girma.
Domin karfafa wannan tsarin na shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida, akwai bukatar shugabannin al’umma a matakai daban-daban su kara fuskantar wannan tsari tare da ba da gudunmawa, wajen wayar da kan al’umarsu, domin aiwatar da shi yadda ya kamata.
Su ma iyaye maza magidanta na da muhimmiyar rawar takawa wajen taimaka wa mata masu raino ta wajen kula da bukatunsu na abinci da na lafiyar jariran da suka haifa musu. Akwai kuma bukatar wadata su da ingantattun abinci da kayan marmari, don taimaka wa murmurewar jikinsu da kara yawa da ingancin nonon da suke shayar da jariransu.
A hukumance kuma akwai bukatar samar da dokokin da za su karfafa gwiwar iyaye mata su aiwatar da tsarin shayar da nonon uwa zalla na wata shida. Misali, ga mata masu aiki a hukomomin gwamnati da masu zaman kansu, akwai bukatar a duba yiwuwar kara tsawon hutun haihuwa daga wata hudu zuwa wata shida; tare da samar da dakin raino a kowace mai’aikata don bai wa mata ma’aikata damar shayar da jariransu nono yadda ya kamata.
Abba Isyaku Adamu, Lamba 1B, Titin Dambazau, Nasarawa GRA, Kano. 08034327142