✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Sharrin Shaidan ne ya sa na kona matata da kaninta’

Ya ce sharrin Shaidan ne ya sa ya aikata Kafin da ake zarginsa da yi

Wani dan kasuwa da ke Jihar Legas da aka kama bisa zargin babbake matarsa da kaninta, Ogudoro Benjamin, ya ce Shaidan ne ya zuga shi ya aikata hakan.

Mutumin, wanda ya riga ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa ya kuma roki afuwa, inda ya ce bai san me ya kai shi yin hakan ba.

Yanzu haka dai Ogudoro na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Legas da ke Yaba, inda ake ci gaba da bincike a kan shi.

Tun da farko dai ofishin ’yan sanda da ke unguwar FESTAC ne ya kama shi, bisa zargin kone matarsa mai suna Chinyere, da dan uwanta mai suna Ifeanyi Edoziem ranar Juma’a a gidansu da ke gundumar Oteyi a Karamar Hukumar Amuwo Odofin ta Jihar.

Bayanai dai sun ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abiodun Alabi, ya ba da umarnin binciko ainihin abin da ya faru.

Lamarin dai ya jefa mutanen yankin cikin fargaba da jimami, saboda sun ce ya faru ne ranar da Chinyere ta dawo daga kasar Scotland.

Nan take dai ta mutu sakamakon kunar da ta samu a jikinta, yayin da shi kuma dan uwan nata ya rasu jim kadan da kai shi asibiti.

Sai dai kafin ya rasu, Ifeanyi ya shaida wa ’yan sanda cewa sun yi wata ’yar sa-in-sa da wanda ake zargin, inda ya yi zargin cewa sun rufe kofa sun hana shi shiga gidan.

Kakakin ’yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama Ogudoro, inda ya ce yanzu haka suna can suna fadada bincike a kan sa.