Kamar yadda sunansa ya nuna, wannan wani littafi ne da aka rubuta da sigar wake, kuma an yi kokari sosai wajen warware jigon da aka nufa da warwarewa. Idan masu karatu ba za su mance ba, mai girma tsohon Shugaban kasar Nijeriya, Alhaji Shehu Shagari ya taba rubuta shigen irin wannan littafin a shekarun da yake malamin makaranta a Sakkwato. Duk da cewa sunan littattafan biyu sun kusa zuwa daya, to amma abubuwan da suka kunsa sun bambanta da juna, musamman tsari da zubin wakokin da ke kunshe cikin su. A yayin da Alhaji Shehu Shagari ya tsara wakensa kacokan game da tarihin Nijeriya gaba daya, shi Dokta Tukur ya tsara nasa wakokin ne musamman bisa abin da ya gani na zahiri game da Nijeriya da kuma zuwan Sarauniyar Ingila, da kuma kiran da ya yi na musamman ga ’yan Nijeriya da su kasance masu kishi da kaunar kasarsu, kamar kuma yadda ya yi yabo na musamman ga shugabannin Nijeriya na farko da bayyana irin yadda suka sadaukar da rayukansu domin daukaka martabar Nijeriya.
Kamar yadda shi Alhaji Shehu Shagari ya kasance malamin makaranta a lokacin da ya yi wannan wake, shi kuwa Dokta Tukur Abdullahi ya kasance cikakke kuma kwararren likita. Don haka, tsabar kishi da sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance ne kawai suka sanya masa zimmar rubuta wannan littafi, duk kuwa da cewa ya shaida mana cewa, yawancin wakokin da ya zuba a littafin nasa, tun yana yaro karami ya rika rubuta su yana adanawa.
Akwai wakoki guda bakwai mabambanta a cikin wannan littafi, kuma an tsara su cikin hikima da ingantattar Hausa. Kowacce na tare da kafiya da hawa da saukar sauti mai kama zuciya. Wake na farko ya sanya masa suna: Lokacin Ziyarar Sarauniya, kuma baituka dari daya da ashirin da bakwai ne ke cikinsu daidai.
Babu shakka an sanya lugga da kwarewar sarrafa harshen Hausa a baitocin waken nan, musamman ga shi mai kwar biyu ne. Dubi dai baiti na shida na waken, inda yake cewa: “A cikin Ikko na ga ’yan Adam/Sai ka ce fara a samaniya.” Malam ka kalli yadda zangon fara ke kasancewa a samaniya, abin ba a cewa komai! Mu duba baiti na goma sha uku, inda yake cewa: “Filin Sukuwa ran nan mutum/A Kaduna, ya ganyen tsamiya.” Tirkashi! Duk wanda ya san yadda ganyen tsamiya ke zuba, zai saurin fahimtar abin da sha’irin nan ke son nunawa. Akwai kuma nishadantarwa a cikin wasu baituka na shi dai wannan waken. Sai mu duba baiti na dari daya da goma sha biyu, inda sha’irin ya bayyana mana irin shagali da bikin da aka yi wa Sarauniya a Legas: “Na ji an ce sun mata bungudu/Wai rawa mai motsa duwainiya.” Lallai Sarauniya ta sha tarba!
Wake na biyu kuwa, ya sanya masa taken Yabon Manyan Najeriya. Wannan waken ya so ya yi kama da waken Marigayi Malam Sa’adu Zungur, Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya? Musamman ta sigar karinsa, sai dai sun bambanta ta bangaren ma’ana da kuma wasa da harshen da sha’iran suka yi. Baituka hamsin da bakwai ne mutum zai samu a cikinta. Sha’irin ya yi kokarin nuna wa jama’a irin namijin kokarin da shugabannin Nijeriya na farko suka yi, da irin kishin kasarsu da suka nuna, da irin son gaskiyarsu, da kuma yadda suka rike amanar jama’arsu. Ya yi yabo ne ga mutane irin su marigayi Sa. Abubakar Tafawa Balewa, da Marigayi Sa. Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, da marigayi Cif Obafemi Awolowo da marigayi Dokta Nmamdi Azikiwe da sauran su. Haka kuma ya jawo hankalin shugabannin yanzu, da su yi koyi da ayyukansu, kuma ya tsoratar da su don su guji cin amanar jama’arsu.
Sai kuma wake na uku, wanda ya yi wa take da, Hada Kai Don Samun ’Yanci. Baituka goma sha tara ne daidai cikin wannan waken, wanda kuma ke dauke da dango biyar-biyar. Kuma akwai wani salo da sha’irin ya yi wa baitocin nan, inda ya rika jera layuka na biyu zuwa na biyar suka gota layukan farko. Wannan wani sabon salo ne mai burgewa. Akwai gargadi, akwai tsoratarwa, akwai nusantarwa da kuma nishadantarwa cikin wannan waken.
A wake na hudu da ke cikin wannan littafi kuwa, an sanya masa suna: ’Yancin Nijeriya, inda sha’irin nan ya yi wa al’ummarmu allurar karin karfi. Ya kawo bayani dalla-dalla na abubuwan da ya kamata duk dan kasa nagari ya rika aikatawa, domin Nijeriya ta kasance cikin ’yanci. Bari mu duba baiti na shida, mu ga irin salon wannan waka: “Ana daga tutar ana kada take/Mai sanya ciwon cikin rai ya narke/Mai sanya duk dan kasarmu ya mike/Ya girmama innarsa Nijeriya.” Baituka talatin ne cif-cif a cikin wannan waken, kuma lallai ya tsaru sosai cikin fa’ida.
Wake na biyar kuwa sunansa, Jamhuriyarwar Najeriya, wanda ke dauke da baituka goma sha uku. Sai kuma wake na shida mai taken, Duniya/Nijeriya, mai dauke da baituka hamsin da takwas. Daga karshe kuma sai waken da ya zama murfi ga littafin, mai suna: Wakar Yabon Manzon Allah (SAW). Yana dauke da baituka casa’in da tara ne daidai kuma sha’irin ya yi hobbasa sosai wajen yabon Dan gatan Allah.
Irin yadda aka yi kokarin tsara littafin nan cikin siga mai tsafta, abin yabawa ne, musamman ma yadda aka zabi kalmomi wadanda suka dace, sannan kuma aka yi gargadi da fadakarwa. Wannan ya sanya da wuya ka samu wata makusa cikin sauri daga littafin. Amma duk da haka, wanda ya nace da nazarin littafin nan zai ga wasu ’yan nakasu kadan nan da can da suka rage wa littafin maki kadan. Za mu dan kawo su nan, domin daidaita nazarin littafin nan. Misali, a baiti na biyu, na waken Yabon Manyan Nijeriya, a shafi na goma sha shida, an rubuta kalmar manyar maimakon manyan. Sai kuma wasu kalmomi da sha’irin ya rika jefawa cikin waken nasa nan da can na Turanci. A ka’idance, tun da da tsagwaron Turancin aka rubuta su, da kamata ya yi a rika sanya su a gicciye (Italics), ba kamar yadda aka rika gwamutsa su da na Hausa ba bai daya.
Haka kuma a waken Duniya/Najeriya, sha’irin ya rika maimaita wannan baitin: La’ilaha illal Lahu/Duniya sarkin canji da yawa a cikin waken kuma bai nuna wa jama’a cewa amshi ba ne. Da son samu ne, da sai ya bar shi daga farko a matsayin amshi, wanda ke nan ba sai ya yi ta nanata shi a cikin sauran waken ba. A cikin Wakar Yabon Manzon Allah (SAW) ma, haka aka sake kwatawa, inda ya rika maimaita wadannan baitukan sau da yawa a cikin waken, duk da cewa bai nuna cewa amshi ba ne; ga su: “Shugaban bayi Muhammadu/Dan Amina mijin Hadija”, da kuma “In ka so shi wuta ta ki ka/In ka ki shi wuta ta so ka.” Baya ga wadannan ’yan abubuwa da na hango, littafin nan bai da wata makusa ko kadan.
Game da sha’irin kuwa, Malam (Dokta) Tukur Abdullahi, cikakken kuma kwararren likita ne, wanda shi ne shugaban asibiti mai zaman kansa mai suna Jinya da ke Kaduna. Haka kuma shi saraki ne, kuma malami. Wadannan baiwa da Allah Ya ba shi, su suka sanya ya kasance wani irin sha’iri wanda ya bambanta da saura ta fuskoki da dama.
Ina kira ga al’umma da su yi kokarin mallakar wannan littafi, domin casar dinbin hatsin ilimin da ya kinshe a cikinsa, domin Shugaban Masu Hikima ya ce, hikima kayan Mumini ce, duk inda ya gan ta, ya dauki abinsa!