Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa.
Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
- Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa
- Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati
Ya ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar da ke Kazaure, Mansur Dabuwa, inda aka lalata katan 400 na barasa da darajar kudinsu ya kai naira miliyan 5.8.
Ya bayyana cewa an kama barasa da aka kona a lokacin samamen da aka kai a sassa daban-daban a yankin.
Kwamandan wanda ya jaddada cewa an haramta shan barasa a duk sassan jihar, ya kuma kara da cewa hukumar za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u da suka hada da shan barasa.
Don haka hukumar ta Hisbah ta bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa hukumar goyon baya da muhimman bayanai domin ta samu damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ya kuma shawarci mazauna garin da su daina aikata miyagun ayyuka da za su iya lalata tarbiyyar al’umma.