Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihar.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafa da ya shirya ga ’yan jarida a fadarsa da ke Karamar Hukumar Potiskum.
Ya ce harin baya-bayan nan da aka kai a yankin Gurjaje da ke Karamar Hukumar Fika ta jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da lalata gidaje sama da 100, ya tabbatar masa da alakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da rashin tsaro.
Sarkin Fika ya bukaci gwamnatin jihar da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta fito da tsare-tsaren da za su dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
- Boko Haram Ta Sake Lalata Turakun Wutar Lantarki Mai Karfin 330KVA A Yobe
- Matsin Rayuwa: An gudanar da sallar neman sauki
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da cigaba a yankunan da lamarin ya shafa, yana mai kokawa kan tabarbarewar tattalin arziki a kasar.