✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shanu za su yi tsada a Binuwai – Shehu Tambaya

Babban Jami’i mai ba Gwamnan Jihar Biniwai shawara game da al’amuran makiyaya dabbobi, Alhajhi Shehu Tambaya ya bayyana cewa shanu da sauran dabbobi za su…

Babban Jami’i mai ba Gwamnan Jihar Biniwai shawara game da al’amuran makiyaya dabbobi, Alhajhi Shehu Tambaya ya bayyana cewa shanu da sauran dabbobi za su yi tsada a Jihar Binuwai, la’akari da yadda Fulani makiyaya ke barin jihar da dabbobinsu, a sakamakon sabuwar dokar hana yawon kiwon dabbobi da ta fara aiki a jihar.

Ya ce ya zuwa yanzu Fulani makiyaya 3,500 daga cikin adadin 6,000 da ke jihar sun yi kaura zuwa wasu jihohin. Ya ce cikin shanu 16,000 mallakin  Fulanin, tuni suka fita da kimanin 10,000 zuwa makwabtan jihohi. Ya kara da cewa makiyayan da suka amince su zauna a jihar ta Biniwai, suna saya wa dabbobinsu abinci ne, maimakon yawon kiwo da suke da su a baya, don haka farashin dabbobi zai tashi matuka a jihar.

“Babu ko shakka, ya zama dole farashin dabbobi ya tashi sama, kuma abin da za a tsammata ke nan,” inji shi.

Sai dai kamar yadda ya bayyana, ba duka Fulanin ne za su kaura daga jihar ba, domin kuwa ya ce a yanzu haka, Fulani makiyaya kimanin 100 sun nuna sha’awarsu na mallakar filaye, inda za su gina wuraren killace dabbobin nasu domin kiwatawa, maimakon yawo da su kwararo-kwararo da sunan kiwo.

Tambaya ya bayyana wa wakilinmu a Makurdi cewa babu shakka wasu makiyayan sun kaura daga jihar da dabbobinsu amma akwai wadanda har yanzu suna nan zamansu kuma sun shirya bin ka’idojin da sabuwar doka ta tanadar.

“A yanzu haka muna kan tattaunawa da shugabannin kananan hukumomi da ke fadin jihar nan, domin su tanadar wa makiyayan da suka zabi zama cikin jihar wuraren da za su mallaka domin ginawa, don killacewa da kiwata dabbobinsu, kamar yadda sabuwar dokar ta tanada.