✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shanu 31 sun yi batan dabo a hannun ’yan sandan Kaduna

Wadansu Fulani sun nemi Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ahmad Abdurrahman su taimaka wajen karbo musu shanu 31…

Wadansu Fulani sun nemi Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ahmad Abdurrahman su taimaka wajen karbo musu shanu 31 da kananan dabbobi biyu da suka yi batan dabo a hannun wadansu jami’an ’yan sandan jihar.

Daya daga cikin Fulanin da aka kwashe wa shanu mai suna Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Habu ya shaida wa Aminiya cewa wadansu ‘yan sanda ne suka je kauyensu mai suna Kaban a Karamar Hukumar Igabi suka kwashe shanun da kananan dabbobi biyu.

Ya ce lamarin ya auku ne wata 12 da suka wuce inda ya ce duk kokarin da suka yi don karbo shanun ya ci tura.

Ya ce, a yanzu lisafin da suka yi na kudin da suka kashe don ganin an sako musu shanunsu ya kai Naira miliyan daya da dubu 700, amma har yanzu ba a ba su shanun ba.

“Lokacin da suka je kauyenmu suka kwashe shanun ba na gida kuma yayana ma ba ya gida, maihafinmu shi ma ba ya gida. Bayan na dawo na samu labarin cewa ’yan sandan sun kwashe mana shanu 31 da tumaki biyu sai yayana da kanena da wani surukinmu suka je wajen ’yan sandan domin bincikar dalilin kwashe mana shanu. Su ma sai ’yan sandan suka tsare su na tsawon kwana 12, har sai da muka yi belinsu a kan Naira dubu 580. Da na yi lissafin kudaden da muka kashe kan karbo shanun nan sun kai Naira miliyan daya da dubu 750, kuma har yanzu ba a ba mu shannun ba,” inji shi

Ya kara da cewa: “Idan mun kira jami’in ’yan sandan da suka je kauyenmu suka kwashe shanun sai ya ce wai shanun suna kotu ko ya ce an kai su Abuja. Saboda haka muke neman a taimaka mana a sako mana shanunmu.”

A kan ko wane dalili ne ’yan sandan suka bayar na kwashe shanun, sai Habu sai ya ce wai suna zarginsa da mallakar bindiga wanda shi kuma ya musanta zargin.

“Wai sun ce ’yan uwanmu ne suka fada musu ina da bindiga, ni kuma na rantse masa a lokacin da muka hadu da shi jami’in ’yan sandan cewa ba ni da bindiga ni ko batirin bindiga ba ni da shi. Daga nan sai suka ce wai bincikensu ya nuna ba ni da laifi amma sai na ba su Naira dubu 700, ni kuma na fada musu cewa ba ni da wannan kudi sai na ba su Naira dubu 200, amma duk da haka shanun ba su fito ba,” inji shi.

Sarkin kauyen Kaban Malam Shehu Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tabbas ’yan sanda sun je kauyen sun kwashe shanun kuma tun daga wannan lokaci har yanzu ba su maido da shanun ba.

Dattijo Alhaji Abdullahi Ibrahim wanda shi ne mahaifinsu Habu kuma shanunsa ne aka kwashe ya bayyana wa Aminiya cewa da ya ziyarci hedkwatar ’yan sandan Kaduna kan maganar shanun a makon jiya sun ce da shi magana na kotu don haka shanu na kotu. “Amma da na je kotun alkalin ya shaida min cewa shanu ba sa kotu kuma shi tuni ya bai wa ’yan sanda umarnin su mai da min da shanuna tun lokacin da aka kai kara gabansa. Saboda haka in koma wajen ’yan sanda su ba ni shanuna,” inji shi.

A kan batun cewa ’yan sanda na zargin daya daga cikin ’ya’yansa da mallakar bindiga wanda hakan ya sa suka kwashe shanun sai ya ce: “Idan suna zargin wani da mallakar bindiga ai ni ba ni ba ne ko, kuma shanuna ne ba na wanda suke zargi ba. Kuma sun ce wai su shanu 28 da kananan dabbobi biyu suka kwashe a gidana. Koma dai nawa ne, ni dai abin da kawai nake so shi ne su mai da min da shanuna,” inji shi.

Kokarin da wakilinmu ya yi don ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo ya ci tura domin ya ce ba zai yi gaggawar cewa komai a kai ba, har sai ya samu cikakken bayani daga sashen CIB da ke binciken lamarin.” Zan kira ka,” inji shi.

Amma har zuwa rubuta wannan rahoto bai kira ba.