✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shan maganin karfin maza ya maida magidanci abin kallo a gari

Saura kiris a yi masa tiyatar kashe mazakutarsa bayan ta ki kwantawa na tsawon kwanaki

An garzaya da wani magidanci asibiti, bayan da ya sha maganin karfin maza, gabansa ya ki kwantawa duk da kokarin ’yan uwa da abokan arziki na shawo kan al’amarin.

Wani kwararren ma’aikacin jinya a Asibitin Kwararru na Sakkwato, Ibrahim Abdullahi, ya ce, saura kiris a yanke shawarar yi wa mutumin tiyata a gabansa, domin sai da suka shafe kwana uku suna jinyar mutumin kafin gaban nasa ya kwanta.

Ibrahim wanda ya ce mutumin ya zama abin kallo  har ga kawayen matansa, ya bayyana cewa “Da ba mu samu nasara ba, za a yi masa aiki ne ta kwanta amma ba za ta sake tashi ba har abada.”

Yaya za ka ji idan da kai ne wannan mutumin, ko a ce mijinki ne hakan ta faru da shi?

Shin me ke sa mutane shan maganin karfin maza?

Yaduwar shan maganin karfin maza

Maganin karfin maza ko maganin kara kuzarin namiji da sauran sunayen da ake kiran su a cikin al’ummar Hausawa, sha da amfani da shi ya zama ruwan dare a wannan yanki na Arewa.

Maganin yana cikin kasuwancin da mutane da dama suke yi wanda kuma ake samun kudi a cikinsa a wannan zamani.

“Wannan lokaci amfani da maganin maza ya yi yawa; Abu biyu nake ganin ya haifar da amfani da maganin, mata da yanayin abincin da muke ci a yanzu.

“Mata a bangarensu suna fifita maganar batsa sama da komai.

“A duk sa’ar da suka hadu a gidajen biki sukan tayar da hirar kwanciya tsakaninsu da mazansu, a nan ne wata za ta ji mu’amala daban da yadda mijinta yake yi mata, sai ta kudirta sai mijinta ya kwanta da ita kamar haka.

“Wata da kanta za ta fada masa ya sha magani don ya yi mata yadda za ta gamsu.

“In kuma tana tsoronsa a cikin matan da suka ba ta labari za ta nemi su samo mata maganin ta sanya wa mijin a abinci ya ci ba tare da ya sani ba, a hakan za ta bi da shi har ya ci gaba da mu’amala da maganin domin kokarin samun gamsuwarta”, in ji Muhammad Inuwa, manazarci kan al’amuran yau da kullum.

Ya ci gaba da cewa, “A gefen abinci kuma da yawa mutane na fadin abincin da muke ci yanzu musamman magi na daskare kuzarin namiji.

“A kokarinsa na gamsar da iyalinsa sai ya koma shan maganin maza, da wuya hukuma ta yi wani abu a kai don ko maganin kiwon lafiya ba a kula da shi yadda ya dace ballantana na maza da ake kallon wani abu ne na ganin dama kawai.

“In da matsalar take har yau ban ji masana sun fadi illar maganin nan karara ba sai dai kame-kame domin ba wani magani da ba ya da illa, tun daga farasitamol, ko an ce maganin maza na da illa, sai mu ce wace iri, don ni mutum daya ne na ji cewa ya makance kan amfani da maganin maza a Jihar Katsina.

“Bayan shi ba wani bayani sai dai ka ji ana cewa suna haifar da ciwon hawan jini ko na hanta ko ciyon rashin tsayawar fitsari.

“Amma a zahiri ka ga illar a wurin mutum dattijo ko matashi babu,” in ji shi.

‘Dalilinmu na shan maganin karfin maza’

Malam Sani mai shekara 50 na cikin masu amfani da maganin, ya ce har yanzu bai san illar da ke tattare da maganin ba, sai dai abin da ya kamata mutane su sani maganin iri-iri ne mai sauki da mai tsada.

Ya ce, “Shan masu araha na Naira 150 ko 100 ko 250 kai da kanka ka san na da illa don sai ka rika jin ciwon kai ko alamun mura, kuma kusan dukkan wadannan aikin yini daya suke yi.

“Wadanda na san suna da kyau na Turawa za ka samu kudinsu ya fara daga Naira 2,500 har zuwa Naira dubu 20, ban san matsalar wadannan ba akwai wanda zai tsaya a cikin jikinka kwana uku wani mako daya ya danganta da jininka,” in ji shi.

Ya yi kira ga mutane su kauce wa magani mai matsala, su rika zuwa wurin likitoci su rubuta musu magani kafin su sha.

Abubakar Aminu mai shekara 39 ya ce, “Ina shan maganin ba ko yaushe ba, sai in yi wata ban sha ba, amma gaskiya kanana nake sha irin su Mai Sulhu da Mai Sasanci da Mai Bunsuru da Mai Bindiga da Mai Zikiri da sauransu, kudinsu 200 ne, wani yakan yi min aikin da nake so wani kuma bai yi ko kadan.

“Gaskiya na fahimci suna da illa shi ne ya sa ba ni mu’amala da su sosai.

“Duk sa’ar da na sha, sai ka ga ba na iya rike fitsari da na ji shi in ban yi ba, zai fara fito min, ba zan samu dawowa daidai ba sai ya fi mako ina haka,” in ji Aminu.

Kasuwancin maganin karfin maza

Malam Haruna Muhammad Dan Tunga, daya daga cikin masu sayar da maganin maza a Tsohuwar Kasuwar Sakkwato, ya ce “Muna sayar da iri-iri na maza da suka kunshi na karin karfin gaba da na shafawa irin su kwayar Bega da Mai.

Akwai wanda ake shigowa da su daga kasashen wajen akwai wadanda ake yi a Kano da Zariya da Katsina, na gargajiya ke nan, a Sakkwato ba a yin maganin maza.

“A fannin saye mutane sun kasu gida biyu, wasu na waje suke so, kwaya ke nan irin Bega ko Black Demond ko Filista wasu kuwa na gida kamar garin magani, irin su Mai Bunsuru ko A Fafata ko Namijin Gaske, ya danganta da abin da kowa yake so da yake ganin zai yi masa amfani a jikinsa,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Wasu mutane abokansu ne ke ba su labarin maganin da suka sha ya yi masu aiki, sai su zo a ba su, wanda zai fara sha kuma yakan zo ya tambaya wanne ne ka ga mutane suna saye sosai, sai ya ce a ba shi, shi ma ya shiga layi.”

Matsalolin shan maganin karfin maza

Game da matsalar da shan maganin ke kawo kuwa, sai ya ce, “Ciwon kai da mutane ke fadi suna samu in sun sha daga jini ne ba mu dauke shi matsala ba.”

Ya ce, “Duk maganin da muke sayarwa sai mun gwada kafin mu fara sayarwa, in suna da matsala mu jingine su domin akwai lokacin da muke bayarwa ga kowane magani.

“Ana kawo yajin maza shi ma muna gwada shi, tsawon lokacin da na yi ban samu maganin da ya kawo min mishkila ba.

“In da ake samun tangarda da mutane in an yi masu bayani su ki bin yadda aka ce, sai ka ga mutum ya ce bai yi masa aiki ba, amma da an gyara masa zai ce ya yi masa tasiri.

“Rashin bin ka’ida ke sa ake kokawa kan maganin,” in ji shi.

Ya ce, “Harkar maganin ta yi min komai muna yin magance lalura gwargwadon hali.”

Muhammad Auwal Abubakar wanda ya ce ya kai shekara biyar yana kasuwancin magungunan, ya ce, “Maza suna sayen maganin daga mu su je su sayar, a yini in akwai kasuwa ina iya tura kayan Naira dubu 100 zuwa 200, a yini kuma ina iya cinikin Naira dubu 20 zuwa 30 har 50 a cinikin gida.

Ya ce, “A nan Sakkwato ba mu da maganin maza kamar su Turmi da Tabarya, daga Kano ake kawo mana su, na mata kawai ake yi a nan.”

Hukuncin masu shan maganin karfin maza

Da yake bayani kan hukuncin amfani da maganin, wani malamin addinin Musulunci, Malam Murtala Da’a ya ce amfani da kayan maza matukar bai saba wa lafiya da cutar da abokin zama ba shari’a ta amince a yi amfani da shi.

“Addinin Musulunci ya zo da bayanin magunguna da yawa kuma ya sanya ka’idoji uku a kan duk wani magani da za a yi anfani da shi.

“Na farko ya kasance halal, ma’ana ba ya cikin abubuwan da Musulunci ya haramta.

Na biyu ya kasance ba ya cutarwa (ga miji ko matar), sannan na uku ya kasance an jarraba sau da yawa an ga anfaninsa.

“Domin ka’idar da take cewa ‘Asalin kowane abu da ake ci ko amfani da shi halal ne sai abin da nassi ya haramta. Allah mafi sani” in ji Malam Murtala.

‘Shan maganin maza na da illa’

Wani kwararren ma’aikacin jinya (Nas) a Asibitin Kwararru na Sakkwato, Ibrahim Abdullahi, ya ce shan maganin maza na da matsala sosai domin shan zai iya haifar da mutuwar gaba ko al’aurar mutum gaba daya.

Ya ce, da yawa ake samun wuce iyaka (over reaction) bayan mutum ya sha maganin mazakutarsa ta ki kwantawa bayan awa 24, wanda hakan ke kai ga mutuwar al’urar.

Ya ce, “A kwanaki an zo mana da wani nan asibitin kan ya sha maganin al’aurarsa ta ki kwantawa a gaban surukansa da kawayen matarsa da ’yan uwansa muka yi ta fama a kansa Allah Ya sa muka yi nasara bayan kwana uku yana jinya kafin ta kwanta.

“Da ba mu samu nasara ba, za a yi masa aiki ne ta kwanta amma ba za ta sake tashi ba har abada.

“Ka ga hakan ko musiba ce da ta kamata mutane su dakatar da kansu da wannan hadari gudun yin da-na-sani.

“Ya kamata hukuma ta shiga lamarin magani musamman na gargajiya domin tsaftarsa da ingancinsa, mafi yawan masu shan maganin marasa ilimi ne ’yan tsakanin shekara 30 zuwa 40,” in ji a Ibrahim.

 

An fara wallafawa ranar 5/11/2022.