Akalla mutum 363 ne suka shiga hannun Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Jihar Jigawa tun daga watan Yuli, 2020 zuwa yanzu.
Alkaluman mutanen da hukumar ta cafke a jihar sun hadar da maza 347 da kuma mata da dama.
Kwamandar NDLEA a Jihar Jigawa, Maryam Gambo Sani ce shaida wa manema labarai cewa Hukumar ta kwato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 344.9 a tsawon lokacin.
Hukumar ta kuma shigar da kararraki 108 a gaban Kotun Tarayya da ke garin Dutse kan ayyukan shan miyagun kwayoyi.
Ta yi bayanin ne a garin Dutse a bikin Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta 2021.
Kwamandar ta ce tun bayan janye yajin aikin ma’aikatan shari’a (JUSUN) wanda suka yi na tsawon wata biyu, hukumar ta samu nasarar mika mutum 30 gaban kotu.
Ta bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su taimaki hukumar wajen yakar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 26 ga watan Yuni, a matsayin Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi a fadin duniya.