✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shakira ta rabu da masoyinta Pique bayan kama shi da lalata da wata mata

Shakira ta kama masoyin nata dan wasan bayan kungiyar Barcelona da wata mata ’yar kasar Spania

Shahararriyar mawakiya ’yar kasar Columbia, Shakira Isabel Mabarak Ripoll, ta kama masoyinta Pique  Periodico, a kan gado da wata mata ’yar kasar Spania.

Matar da Shakira ta kama masoyin nata da ita a kan gado, ma’aikaciya ce a gidan jarida na El Periodico da ke Barcelona a kasar Spania.

Masoyin na Shakira, Pique Periodico, shi ne mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

Pique da Shakira sun fara soyayya da juna ne bayan fitowarsa a bidiyon wakarta ta Gasar Kwallon Kafa ta Duniya ta 2010, mai taken ‘Waka Waka’, a shekara ta 2010.

Tun daga 2011 dai suka fara soyayya kuma suke tare da juna, sai dai ya zuwa yanzu ba su yi aure ba.

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu masoyan sun yanke shawarar rabuwa, inda Pique zai ci gaba da zama a gidansa shi kadai.

Masoyan biyu dai na da ’ya’ya biyu da suka hada da Sasha da Milan.