✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shakatawa ce ta kai ni Amurka ba jinya ba — Gwamna Sule

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya musanta zargin da ake yi masa na cewa a yanzu haka ya fita neman magani ne a Kasar…

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya musanta zargin da ake yi masa na cewa a yanzu haka ya fita neman magani ne a Kasar Amurka, yana mai jaddada cewa ya ziyarci Amurkan ne domin ganin ’ya’yansa a yayin da yake hutunsa na shekara.

Ya yi wannan karin haske ne a yayin da ya bayyana a matsayin bako a wani shiri da gidan talbijin na Channels ya watsa a birnin Lafia.

Gwamnan wanda ya dauki zargin da ake yi masa a matsayin raha, ya yi bayanin cewa ya saba tafiya hutu duk karshen shekara a watan Dasumba, kuma yana amfani da wannan dama ya ziyarci iyalinsa a garin Houston na Jihar Texas da ke Amurka.

Gwamna Sule ya ci gaba bayar da bayanin cewa, a yayin da yake hutu a Amurka kamar yadda ya saba tun a baya, yana kuma amfani da wannan dama ya rika zuwa ana bincikar lafiyarsa lokaci zuwa lokaci.

“Ya kamata al’umma su sani cewa balaguron da na yi zuwa Amurka ba ya da wata dangantaka da rashin lafiya, shakata wa ta kawo ni garin Houston kamar yadda na saba duk shekara idan na dauki hutu, kuma na kan yi amfani da wannan dama na ga likitoci na domin a binciki lafiyata.”

“Dama can na kan zo a duba lafiyata tun a lokacin da nake Manajan Darakta a Kamfanin Dangote. Saboda haka lafiyata kalau, don ba a dade da bincikar lafiyar hakora na da idanu ba, kuma an tabbatar garau nake,” inji Gwamnan.

Yayin da yake ci gaba da watsi da jita-jitar cewa jinya ce ta kaishi Amurka, Gwamna Sule ya ce yana da Likitansa a Gidan Gwamnati wanda ke duba lafiyarsa a kai a akai, kuma ko a kwanan nan, matarsa ta haifi tagwaye a wani Asibiti a birnin Abuja.

Ya ci gaba da bayanin cewa tunda har ta kasance yana da iyali da ke zaune a Houston, duk lokacin da ya ziyarci Amurka galibi a watan Dasumba yayin hutunsa na shekara-shekara, ya kan yi amfani da wannan dama wajen ganin likitinsa da suka dade tare domin a binciki lafiyarsa.

 

%d bloggers like this: