Da yawa daga cikin shahararrun ’yan kwallo a Nahiyar Turai suna amfani da damar da suka samu wajen mallakar kulob na kashin kansu. Wadansu sukan mallaki kulob din ne da zarar sun yi ritaya, yayin da wadansu ma tun kafin su yi ritayar suke mallakar kungiyoyin kwallon kafa a sassan duniya. Kan haka ne Aminiya ta yi nazari game da irin wadannan ’yan kwallo da kulob-kulob din da suka mallaka kamar haka:
1. Dabid Bechkam: Dabid Beckham dai shahararren dan kwallon kafa ne. Dan asalin Ingila, ya buga wa shahararrun kulob da dama a ciki da wajen Ingila. Yana daga cikin ’yan kwallon da kulob din Manchester United na Ingila ba zai taba mantawa da su ba, musamman kan gudunmawar da ya bayar wajen daukaka martabar kulob din. Sannan ya taba buga wa kulob din Real Madrid na Sifen kafin ya koma Amurka don ci gaba da kwallo. A shekarar 2007 ne ya koma kulob din LA Galazy da ke Amurka. A lokacin da yake kwallo a Amurka ne ya samu damar saye kulob din Inter Miami na Amurka a kan Dala miliyan 25 kwatankwacin Naira biliyan 9. Duk da haka ya samu rahusa wajen saye kulob din saboda an yi gwanjon kulob din ne. LA Galazy na daga cikin manyan kulob din da ake ji da su a Amurka, don an sha rade-radin manyan ’yan kwallo irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suna da sha’awar yin wasa a kulob din idan suka samu damar yin hakan.
2. Ronaldo: Akwai yiwuwar wadansu su yi tunanin wane Ronaldo ake nufi, na Brazil ko na Fotugal? Ronaldo Nazario, shahararren dan kwallon Brazil ne da ya buga wa manyan kulob da dama da suka hada da Real Madrid da FC Barcelona na Sifen da Inter Milan na Italiya. Dan kwallon ya sayi hannun jari a kulob din Fort Lauderdale Strikers da ke Amurka ne a shekarun baya sannan a bana (2018) ya sake mallakar kashi 51 daga cikin 100 na kulob din Real Balladolid da ke Sifen. Yanzu haka kulob din ne na 7 a teburin gasar La-Liga ta Sifen. Za a iya cewa Ronaldo ne dan kwallo na farko da ya mallaki hannayen jari a kulob biyu a kasashe daban-daban. Baya ga harkar kwallon kafa an ruwaito dan kwallon ya zuba jari a bangaren wasan kwallon kwando da na tseren mota da sauransu.
3. Eden Hazard da Yohan Cabaye da Demba Ba da Moussa Sow: Dukan wadannan ’yan kwallo da aka lissafa sun hada karfi ne wajen mallakar wani kulob mai suna San Diego 1904 da ke Amurka. A bara (2017) ne aka kafa kulob din inda ’yan kwallon suka hada karfi wajen mallakar kulob din da ya zama nasu na kashin kansu.
Eden Hazrd, dan kwallon kulob din Chelsea wanda ya fi yin fice a cikinsu, ya bayyana farin cikinsa game da mallakar hannun jari a kulob din a wata hira da manema labarai suka yi da shi a Amurka a kwanakin baya. Kulob din dai yana wasa ne a gasar rukuni na 3 na ’yan dagaji a Amurka.
4.Paolo Maldini: Paolo Maldini, tsohon dan kwallon kulob din AC Milan da ke Italiya ne. Yana daga cikin wadanda suka daukaka martabar kulob din a lokacin da yake kwallo.
Rahotanni sun nuna Maldini ya hada gwiwa ne da wani shahararren dan kasuwa a Amurka Ricardo Silba wajen mallakar kulob din Miami FC da ke Amurka. Shi ma ya shiga kundin tarihi a matsayin dan kwallon da ya mallaki kulob na kashin kansa.
5. Paul Scholes da Nicky Butt da Ryan Giggs da Gary da Phil Nebille: Dukan wadannan ’yan kwallo sun yi wa kulob din Manchester United na Ingila kwallo.
Hasali ma ’yan kwallon ne aka ganin kulob din Manchester United yake ji da su a 1992. Sun hada gwiwa ne wajen mallakar kulob din Salfod City da ke Ingila. Kulob din yana wani gari ne da ke kusa da Manchester a Ingila.
Sai dai an ruwaito sun sayar da hannun jarin kashi 50 daga cikin 100 na kulob din ga mai kulob din Balencia na Sifen, Peter Lim a ’yan shekarun baya lokacin da suka fahimci kulob din yana fuskantar kalubale. Yanzu dai za a iya cewa wadannan ’yan kwallo da Peter Lim ne suka mallaki kulob din Salford City da ke Ingila kuma sun shiga kundin tarihi a matsayin wadanda suka yi kwallo sannan suka mallaki kulob na kashin kansu.
6. Didier Drogba: Dan asalin Kwaddibuwa, Didier Drogba ya kafa tarihi a matsayin bakar fata na farko da ya fito daga Nahiyar Afirka sannan ya mallaki wani kulob a Amurka. Drogba, wanda ya yi kwallo a kulob da dama, ya fi shahara ne a lokacin da yake buga wa kulob din Chelsea da ke Ingila wasa. Ya taba zama Gwarzon Dan Kwallon Afirka, sannan ya taba lashe kyautar dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye a gasar Firimiyar Ingila. Jim kadan bayan ya koma Amurka da buga wa kulob din Phoenid Rising sai mahukunta kulob din suka yi masa tayin mallakar kulob din. Bai bata lokaci ba ya amince kuma ciniki ya kaya. A lokacin sai ya zama yana daya daga cikin ’yan kwallon kulob din, kuma shi ne shugaba. Ke nan yana jifar tsuntsu biyu da dutse daya.
Da tafiya ta yi nisa sai ya ga ba zai iya hada taura biyu a baki ba, inda ya yanke shawarar daina buga wa kulob din ya mayar da hankali wajen tafiyar da harkokin kulob din a matsayinsa na shugaba.
Yanzu haka Drogba yana tafiyar da harkokin kulob din Phoenid Rising a matsayinsa na shugaba, kuma ya zama bakar fata na farko a Nahiyar Afirka da ya mallaki wani kulob a Amurka.