✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shagwaba ‘ya’ya na lalata tarbiya – Dokta Hafsatu Shehu

Rayuwarta: An haifen nei a 1965 a garin Yola sunan mahaifina Malam Ummaru, mahaifiyata Malama A’isha.   Na yi karatun firamare a Waje Primary School,…

Rayuwarta:

An haifen nei a 1965 a garin Yola sunan mahaifina Malam Ummaru, mahaifiyata Malama A’isha.   Na yi karatun firamare a Waje Primary School,      Bunza na Jihar Sakkawato daga 1972 zuwa1978 daga nan na wuce Kwalejin ’yan mata ta gwamnatin tarayya  FGGC Yola daga1978 zuwa1983, sai na koma gida don a gidanmu ba a kara karatu sai an yi aure.   Bayan na yi aure ne mijina ya ga takarda ta ta yi kyau sai ya nema min Kwalejin Horar da Malamai (COE) da ke Sakkwato a tsakanin shekarar1984 zuwa1987.  A can ne na samu shaidar malanta ta kasa (NCE) da na kare sai na fara karantarwa a makarantar tunawa da Ahmadu Bello da ke Farfaru  daga nan na koma digiri na farko a Jami’ar Usman danfodiyo dake Sakkwato a fannin ilmin itatuwa da tsirrai da abubuwan da suka shafe su  (UDUS- B Sc Botany a tsakanin shekarar 1991 zuwa1996) bayan na kammala sai na koma na yi digiri na biyu da na uku a duk a Jami’ar danfodiyon da ke Sakkwato wayau na samu shaidar karatu ta (M. Sc Botany a 2004 da kuma Ph. D. Botany a shekarar 2016).

Aiki:

Na yi ayyuka a wurare da dama da suka hada da Ma’aikatar ilimi ta Jihar Sakkwato (Ministry of Education) a matsayin malama inda aka tura ni Makarantar yara taAhmadu Bello Academy Farfaru da ke Sakkwato a tsakanin shekarar 1989 zuwa 1999 daga nan na koma koyarwa a wata Kwaleji ta musamman da ke karkashin Jami’ar Usman danfodiyo (Usmanu danfodiyo Unibersity Model Secondary School) a tsakanin 1999 zuwa 2007 daga nan na ci gaba da koyarwa a Jami’ar Usmanu danfodiyo a Department of Biological Sciences tun daga 2008 kawo yanzu.

Mukamai:

Daga cikin mukaman da na rike sun hada da Shugabar sashen kula da karatun yara (Form Mistress) naAhmadu Bello Academy da ke Jami’ar Usmanu danfodiyo da ke Sakkwato.  Sannan na rike shugabar sashen karatun Tsirrai  (HOD Biology) na rike shugabar sashen Kimiyya (HOD Sciences) a Kwalejin Yara ta Usmanu danfodiyo Model Secondary School.  Sannan na rike Mataimakiyar Shugabar Kwalejin a tsakanin 1999 zuwa 2001 da Mataimakiyar Shugabar Kwalejinj bangaren karatu a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004 daga nan na zama shugabar Kwalejin watau Principal a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2008.

Kwamitocin da na yi aiki a ciki sun hada da:

Mamba a Kwamitin Gudanarwa na Jam’iar Usmanu danfodiyo da ke Sakkwato a tsakanin shekarar 2013 zuwa yau.  Sannan ni mamba ce a Kwamitin sanya ido game da yadda ake gudanar da jarrabawa a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015, sannan na kasance mamba a kwamitin tantance sahihancin takardun dalibai a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015.  Haka kuma na kasance memba a kwamitin hana cin hanci da rashawa na Jami’ar Usmanu danfodiyo a tsakanin shekarar 2016 har zuwa yau.  Sannan na kasance mai kula da yadda dalibai ke kokarin sanin makamar aiki (SIWESS) tun a shekarar 2015 zuwa yanzu.

Nasarori: 

To na samu nasarori a rayuwa da dama amma  kafin nan na hadu da kalubale masu yawa.  Kowa ya san ba a abu ba ne dake da sauki ba hada karatu da rayuwar aure amma na samu nasara.   Da danyen goyo na kammala karatun NCE.   Sannan na fara karantarwa ne a wata makarantar maza inda aka tura ni  ajin manya har sun fara turjewa sai na dauki matakin ladabtarwa sannan suka zama daidai.   Da na koma Kwalejin jam’i’a a matsayin Mataimakiyar Shugabar Kwalejin ana dauka ta a matsayin mai tsanani ga yara da uwayensu amma da yara suka samu nasarori a jarabawarsu abin ya koma farin ciki.  Da na zama shugaba kuma sai na kashe zuwan yara aji na gaba don kawai su rubuta jarabawa fita ba tare da sun kai can ba sai ga shi a shekarar da muka hana duk yaron da ya rubuta jarabawar fita sai da ya samu gurbin karatu a jami’a nan ma uwayensu suka yaba wannan don niyyata kawai na taimaki dalibai su samu guraben ci gaba da karatu. 

Burinta a rayuwa: 

Burina na rayuwa ya cika don kowa na son abin da ya sanya a gaba ya samu nasara a lokacin ina karama Burina na yi karatu to a yau ina da karatun digitin-digirgir (Ph.D)  Ni Dokta ce don haka burina ya cika, da zarar na yi magana za a saurare ni, to ka ga wannan ba karamin nasara ba ce a rayuwa.

Abin da take so a rika tunata da shi:

To ni dai almajira ce kuma malamar Makaranta, duk wanda zai tuna ni to ya tuna da abubuwan da na yi na alheri a lokutta da dama.   Mutum zai karantar da yaro ba tare da an biya shi ba, zai yi masu nasiha da wa’azi da ba su tarbiyya duk lamarin ladabi na makaranta ni ce gaba ina son a tuna da ni a matsayin malamar makaranta. 

Yawaitar mata a makarantu:

A gaskiya in ka duba yadda ake barinsu zuwa makaranta a baya, a yau ya fi inda aka fito don an yi kokari  amma akwai sauran gibi don a cikin birni ne kawai ake zuwa makaranta in ka tafi kauye ba sa zuwa karatun boko da na  Islamiya, Ko iyayensu ba sa da kudi ne ko ba sa bukatar yaran su yi karatu don gudun zama marasa tarbiyya? Wasu kuma ba sa sanya yaransu makaranta ne saboda rashin tsaro.  Wasu har sun sanya yaran suka cire su, don haka akwai bukatar a rika wayar da kan irin wadannan iyaye don su san muhimmancin sanya ’ya’yansu a makaranta.

Tarbiyyar mata a yau:

Akwai banbancin yanzu da a shekarun baya.   In yarinya ta yi abu mara kyau wanda ba na kusa da ita ba ma zai yi mata fada kuma ta dauka amma yanzu ba dama wani ya yi wa dan wani fada iyaye ba su bai wa ’ya’yansu tarbiyyar da aka ba su ba. Mun bi ra’ayin yaran ga abin da ba daidai ba.   Za ka samu yarinya ce a gida ba ta aikin komai, ba su karatu wai ana gudun yi masu magana.  Yanzu mu ke tsoronsu,  ga wayar hannu ma ta janyo mana matsala da yawa kuma tana nan tana yi ga abubuwa nan ba sa lissafuwa.   Duk abin da suka tambaya ana ba su, ba a la’akari da tarbiyyar abin da kuma yiun nazari kafin a ba su.  Mun taimaka wajen rugujewar auren ‘ya’yanmu don an nuna masu rayuwar jin dadi, don haka wasu ba su san babu ba.  Tilas iyaye mu tashi tsaye don ganin mun samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yanmu. 

Kungiyoyin da take ciki:

kungiyar harkokin addinin Musulunci (MSO) kadan nake ciki.  Amma na ji dadin ziyarar da na kai kasar Saudiyya.